Gwamnatin Gombe Za Ta Bunkasa Kiwon Lafiya Ga Jama’arta

Kiwon Lafiya

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yin hadin gwiwa da Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, (UNICEF) a dukkan fannonin da suka dace wajen ganin an samu nasarar cimma burin kula da lafiya ga kowa.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilin asusun na UNICEF a kasar nan, Mista Peter Hawkins a gidan gwamnati. Ya ce gwamnatinsa tana fatan kulla alaka mai karfi da Gwamnatin Kasar China don bunkasa sauran fannoni kamar na noma da hakar ma’adanai da makamashi da sauran su.

 

Ya kuma bayyana godiya ga asusun UNICEF da gwamnatin kasar China bisa hadin gwiwa da goyon baya da suke bai wa Gwamnatin Jihar Gombe wajen inganta wasu cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda 10 a karamar hukumar Kwami da ke jihar.

 

Kamar yadda Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe, ya nakalto cikin wata sanarwa, gwamnan ya ce tallafin ya tabbatar da burin gwamnatinsa na samun akalla asibitin kula da lafiya matakin farko guda daya a kowace gunduma cikin gundumomi 114 na jihar.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatinsa ta yi kokari sosai a fannin lafiya, amma idan aka yi la’akari da girman jihar akwai bukatar a fadada shirin zuwa sauran kananan hukumomi, inda ya ce idan aka kara fadada shirin, zai bai wa gwamnatin jihar damar cimma burinta a sashin kiwon lafiya.

 

Ya bayyana cewa a halin yanzu Gombe tana samar da abinci kyauta ta hanyar hadin gwiwa da cibiyar bincike a sashin noma.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce kasancewar ta a tsakiyar Arewa maso Gabas, jihar tana ci gaba da daukar nauyin ‘yan gudun hijira da dama wadda hakan ke yin tasiri kan samar da ayyukan jin dadin jama’a.

 

Tun farko a jawabinsa, wakilin asusun na UNICEF na kasa, Peter Hawkins ya bayyana hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da UNICEF a matsayin mai matukar muhimmanci wajen ganin an samu ci gaba mai dorewa a jihar.

 

“Daga abin da na gani dangane da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jama’a a matakin kasa, kun samar da yanayi mai kyau don hakika an fara gudanar da ayyuka masu inganci wanda shi ne muhimmin al’amari, domin jama’a za su ci gaba da zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin samun kulawa”.

 

Ya ce, gyaran cibiyoyin kiwon lafiya da Gwamnatin Jihar Gombe da hadin gwiwar UNICEF da China suka yi, ya sake jaddada bukatar dawwamammen hadin gwiwa a tsakaninsu.

 

Shugaban Asusun na UNICEF ya taya Gwamna Inuwa Yahaya murnar samar da tsarin samar da ci gaba na shekara goma, inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga jihohin kasar nan da kuma masu fada a ji a yankin da ke da matukar bukatar zuba jari da wadata al’umma.

 

 

Exit mobile version