Daga Khalid Idris Doya
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sha alwashin daukan mataki domin magance matsalar da sansanin matasa masu yi wa kasa hidima na jihar Gombe ke ciki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakwancin mambobin gudanarwar hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC karkashin jagorancin shugabar tawagar Ambasada Fatima Balla Abubakar.
Ya ce, “Kamar yadda aka sani sansanin da gwamnatin tarayya ta karba shekaru da suka gabata, an karbe shi ne don yin amfani da shi na watanni 6 kacal, amma a yanzu an shiga shekara ta 5 ba tare da wani yunkuri daga gwamnatin tarayya kan makomar sansanin ba”.
Gwamnan ya ce don haka gina wani sabon sansanin zai lashe kudade da dama, duba da cewa Naira miliyan dari shida aka kashe yayin gina na Malam Sidi Shekaru 12 da suka gabata, wanda ya ce tuni ya mika wannan korafi ga shugaba Buhari yayin wata ziyara, inda ya ce yanzu ana jiran amsa ne kan mataki na gaba da za a dauka.
Ya kara da cewa, “Saboda haka muna matukar bukatar sansanin, yayin da hukumar NYSC ta tallafa mana wajen bunkasa malamai da sauran ma’aikatan gwamnati, saboda haka za mu ci gaba da kokari idan muka samu aka ba mu diyya sai mu gina wani”.
Yayin da ya ke bada tabbacin kare matasan masu yiwa kasa hidima bayan barkewar Korona, Gwamna Inuwa ya bayyana cewa duk da matsalar da ake fuskanta wajen tura ruwa daga madatsar ruwa ta Dadinkowa, amma za a tabbatar da samar da ruwa ga sansanin dake Amada.
A na ta bangare, shugabar sashin gudanarwar hukumar ta NYSC Ambasada Fatima Ballah Abubakar ta bayyana cewa sun zo Gombe ne domin duba sansanin masu yi wa kasa hidima na jihar tare da neman tallafin gwamnan game da matsaloli da sansanin ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin magance su.
Ta na mai cewa wassu daga cikin matsaloli da suka gani sun hada da rashin isasshen wajen kwana ga matasan da kuma karancin ruwa.
Sai ta yaba wa gwamnatin jihar da bisa tallafawa harkokin hukumar, ta na mai bukatar gwamnatin ta kaiwa sansanin dauki.