Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya mai ci a jihar Gombe ta hannun hukumar kula da ilimin bai-daya daga tushe ta jihar wato SUBEB, za ta yi kwaskwarimar babbar makarantar sakandaren jeka ka dawo ta Comprehensibe dake Deba, da karamar makarantar sakandaren garin Dadinkowa duk a karamar hukumar Yamaltu-Deba.
Za dai a sake ginin rukunin azuzuwa guda 16 ne a makarantar sakandaren ta Deba da aka yi kiyasin za su lashe kudi Naira miliyan 45, yayin da karamar makaratar sakandaren ta Dadinkowa kuma za a yi mata kwaskwarima, baya ga gina sabon dakin rubuta jarrabawa dana girka abinci, da dakunan kwanan dalibai, da samar da ruwa da wutar lantarki da aka yi kiyasin za su lashe kudi naira miliyan 126.
Da ya ke jawabi yayin mika wuraren ayyukan 2 ga ‘yan kwangilan, kwamishinan ilimi na jihar Gombe Dakta Habu Dahiru ya gargade su cewa Gwamnatin Jihar ba za ta lamunci aikin ha’inci maras kargo ba.
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Inuwa ta kammala shirye-shiryen gina makaranti na musamman guda 5 a jihar a kananan hukumomin Gombe, da Akko, da Kaltungo da Yalmatu/Deba da kuma Dukku.
Ya ce “Wadannan makarantu za su kasance na zamani dauke da wadatattun kayan aikin koyo da koyarwa da kwararrun malamai don samar da hazikan dalibai na musamman”.
Don haka ya bukaci malamai a jihar su guji dabi’ar kin shiga aji, yana mai cewa duk malamin da aka kama da wannar dabi’a to ya kuka da kansa.
Tun farko a jawabinsa, shugaban hukumar ta SUBEB Honorable Babaji Babadidi, ya ce abun takaici ne ganin yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta bar makarantu suka lalace ba tare da kulawa da su ba.
Sai ya yaba wa Gwamnatin mai ci ta Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa kafewa da tsayuwar dakan ta na ganin an kyautata dukkannin makarantin jihar.
Ya ce, “Bada kwangilan sake gina wadannan makarantu wata babbar nasara ce ga wannar gwamnatin ta Muhammadu Inuwa Yahaya wacce ta himmatu wajen farfado da sashin ilimi. A matsayi na na wanda na taba zama Darakta a ma’aikatar ilimi, na ga ayyukan farfado da ilimi kala-kala, amma ban taba ganin wanda ya yi ko kusa da wannan ba”.
Shugaban karamar hukumar Yalmatu Deba Honorable Shuaibu Umar Galadima, ya gode wa gwamnan na Gombe bisa ceto wadannan makarantu da gwamnatin baya ta yi watsi da su.