Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gwamnatin Gombe Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da NNPC Kan Samar Da Mai Daga Tsirrai

by Muhammad
January 24, 2021
in LABARAI
2 min read
Tsirrai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da damar da kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) ya samar don bunkasa makamashin da ake iya sabuntawa a kasar nan.

samndaads

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi babban Manajan sashin makamashin da ake iya sabuntawa na kamfanin Man na NNPC Dakta Dabid Balarabe Ture, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa rangadin zuwa wuraren da aka tsara samar da makamashin daga rake a Jihar Gombe.

Gwamnan ya ce matakin gwamnatinsa na kafa kwamiti kan makamashin da ake iya sabuntawan ya biyo bayan tattaunawan sa ne da tsohon babban Manajan kamfanin na NNPC na wannan sashi, lamarin da ya ba shi kwarin gwiwan daukan kyakkyawan matakai na aiwatar da wannar aniya.

Ya ce; ‘‘Kuma muna da yakinin cewa idan muka cimma wannar manufa, akalla za mu iya magance babbar matsalar da kamfanonin mu ke fama da shi ta fuskar makamashi. Bisa bayanan da na samu, za mu iya samar da wuta mai karfin Megawatt 60, wanda za ta iya wadatar da al’ummomin arewa maso gabas baki daya’’.

Gwamnan ya kuma yi maraba da shawarar cewa gwamnatin sa ta sake nazartar yanayin aiwatar da shirin dama irin tasirin da hakan zai yi ga muhalli.

Ya ce, ‘‘Na san a sama can, manya irinku dama shi kansa babban Manaja kuna da sha’awar ganin wannan shiri ya tabbata, haka nan lokacin da na ziyarci shugaban kasa, mun tattauna wannan batu. Kuma kun san cewa kasar da muke da ita kama daga ‘Dadin Kowa’ zuwa Gombe Abba kasar noma ce mai kyau da za a iya noman rani a kanta, don haka banga dalilin da zai hana mu yin amfani da ita ba don bunkasa harkokin noman mu da sauran damammakin da za su amfani talakawa.”

Ya ce duba da irin muhimmancin da gwamnatinsa ta baiwa wannan batu na samar da mai daga rake, zai ci gaba da bibiya da sanya ido shi da kansa don tabbatar da nasaran shirin.

Gwamna Inuwa sai ya yi amfani da damar wajen bayyana godiyar sa ga hukumar bunkasa rafin Benue, yana mai cewa gwamnatin sa da hukumar dama wassu da dama suna aiki tare kan cimma wannan buri.

Sai ya yaba da irin hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin uku, yana mai cewa irin wannan hadaka za ta taimaka wajen bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jihar Gombe.

Babban Manajan kamfanin sashin makamashin da ake iya sabuntawa Dakta Bala Ture, ya ce duk da kokarin da aka yi tsawon shekaru 15 da suka gabata, kusan ba wani ci gaba da aka samu ta fuskar aiwatar da wannan shiri a Jihar Gombe.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gidauniyar Ogan Boyen Kwankwasiyya Da “YOMPON” Sun Ba Marasa Lafiya 1,500 Magani Kyauta A Kaura Goje

Next Post

Bude Kan Iyakokin Kasar Nan Zai Amfani Kungiyar NATA

RelatedPosts

Sarkin Musulmi

Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne –Sarkin Musulmi

by Muhammad
17 hours ago
0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce...

Sulhu Da Masu Garkuwa: Gwamnatin Zamfara Ta Amso Mata Takwas Da ‘Ya’yansu

Sulhu Da Masu Garkuwa: Gwamnatin Zamfara Ta Amso Mata Takwas Da ‘Ya’yansu

by Sulaiman Ibrahim
22 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, Gusau A shirin Gwamnatin Jihar Zamfara na...

Gwamnatin Zamfara Ta Amshi Tubabbun ’Yan Bindiga Uku

Gwamnatin Zamfara Ta Amshi Tubabbun ’Yan Bindiga Uku

by Sulaiman Ibrahim
22 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed, Matawallen...

Next Post
NATA

Bude Kan Iyakokin Kasar Nan Zai Amfani Kungiyar NATA

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version