Abubakar M Tahir" />

Gwamnatin Jigawa Za Ta Tura Dalibai  Mata Koyo Aikin Likita A Kasar Waje

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagoranci Muhammad Badaru Talamiz ta sanar da cewa zata tura zunzurutun yan mata yan kasa da shekara 23 kasar waje domin karantar likitanci.

Haka na kunshene cikin ganawar da sakataren hukumar lafiya na jihar Dr.Salisu Muazu yayi da yan jaridu a birnin Dutse.
Dakta Salisu Muazu ya bayyana cewa daliban mata wanda keda raayi zasu iya tura takardun karatunsu ofishinsa dake ministary din lafiyar jihar daliban su kasance yan kasa da shekara 23  kuma su kasance sun zami kiredit biyar ciki kwa akwai lissafi da turanci.
Ya bayyana cewa, dole ya zama yar asalin jihar jigawa kuma zaa fara karbar takardun daga  ranar 12 zuwa 18 ga wannan watan na fabareru. Zakuma ga gudanar da jarabawar daukan ranar 18 ga wata.
Ko a kwanakin baya jihar jigawa ta dauki daliban 60 maza ta turasu kasar  waje karantar likitanci.
Haka kuma shekaru hudu da suka gabata ta tura wasu daliban kasar chaina inda suna gab dawowa gida bayan zama kwararrun likitoci.

Exit mobile version