Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home KIWON LAFIYA

Gwamnatin Jihar Bauci Ta Rufe Asibitoci 18, Sha-ka-tafi 117

by Tayo Adelaja
September 12, 2017
in KIWON LAFIYA
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Hukumar lafiya ta jihar Bauci ta bayyana cewa ta sanya wani kwamiti mai karfin gaske wanda ya zaga asibitoci da kuma shagunan magani (sha-ka-tafi) masu zaman kansu da suke fadin jihar domin yin dubiya da kuma shawo kan matsalolin da suke jibge a asibitocin domin shawo kan matsallolin da suke fuskanta, domin inganta lafiyar al’umman jihar.

Asibitocin da kwamitin ya bincika don tsaftace baragurbi da kuma ‘yan bunburutu sun hada da kananan asibitocin jinyan cuta daban-daban, da suka hada da asibitocin hakori, ido, asibitocin amsar haihuwa, da kuma asibitocin da suke duba cutar kunne. Haka kuma binciken bai tsaya haka ba, kwamitin ya kuma duba asibitocin da suke gwaje-gwajen jini, da kuma na daukan hoto da sauransu a dukkanin fadin kananan hukumomi 20 na jihar Bauci. Haka kuma, sun bincika shagunan saida maganin jinya a fadin jihar.

Jimkadan bayan mika rahoton kwamitin, kwamishina a ma’aikatar lafiya na jihar Bauci, Hajiya Halima Mukaddas ta bayyana cewa nan take ta bada umurnin rufe asibitocin 18 da kuma sha-ka-tafi 117 da ba su cika sharuddan kafa asibitocin nasu ko kuma kula da marasa lafiya ba. inda ta ce, nan take sun rufe asibitoci kwara 18 daga cikin asibitoci 160 da kwamitin ya tsaftace. “Daga cikin asibitoci 160 da aka bincika, mun baiwa asibiti 42 izinin ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda suke yi. asibitoci 23 kuma masu ‘yan kananan matsaloli mun basu umurnin su gyara matsalolinsu. Sai kuma wasu asibitoci 21 da muka ce sai sun gyara matsalolinsu kuma mun shaida sun gyara, haka kuma asibitoci kwara 12 da muka dakatar da su daga kula wasu fanni na jinya sakamakon rashin samar da wasu kwararru a fanonin da suke kulawa. Sannan kuma nan take mun rufe asibitoci kwara 18 inda muka dakatar da su daga dukkanin harkokin lafiya ya zuwa yanzu”.  In ji ta.

Kwamishiniyar ta ci gaba da cewa sun kuma dakatar da shagonan saida magani kwara 117 daga cikin 278 da suka samu sahalewar hukumar nata.

Halima Mukaddas ta bayyana cewa daukar wannan matakin ya zama dole, la’akari da cewa ana samar da asibiti ne domin waraka ba wai don kara wa majinyaci cuta ba; a bisa haka tace matakur asibiti bai cika sharadin da aka gindaya masa ba, mafi a’ala kawai a rufesa har zuwa lokacin da zai cika sharadin da ya kamata, da kuma samar da kayayyakin ayyukan da suka kamata.

Mukaddas ta bayyana cewa, tun asuli wasu daga cikin asibtocin da suka rufe ma ba su samu tantancewa da kuma basu izinin budewa daga hukumar lafiya na jihar ba, inda ta ce kofarsu a bude take ga dukkanin mai son cika sharadin suna saida form din arha a ma’aikatar.

Kwamishiniyar lafiyar ta kuma bayyana cewa, ga masu daukar magani a hanunsu suna fakewa da saida magani inda suke saida miyagun kwayoyi ta bayyana cewa, su irin wadannan nan take kame ne ya dace da su ba zallar rufewa ba.           Da take magana kan ci gaban aikin kwamitin kuma, kwamishiniyarta bayyana cewa, wannan kwamitin, kwamiti ne na dindindin wanda zai ci gaba da yin aikinsa a sauran yankunan da ba duba ba; ta ce har cikin karkara kwamitin nan zai duba gami da jewa domin tantancewa, “Masu saida kayan maye muna ci gaba da tattaunawa don yadda zamu shawo kan wannan matsalar. Matsalace da ta shafi janibobi da dama”. Injita

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Bankin Bunkasa Noma Da Ruwa Zai Kashe Dala Biliyan 400 A Fadin Kasar Nan

Next Post

Jami`an Kananan Hukumomin Jahar Yobe Sunyi Taron Tattaunawa Akan Cutar Foliyo A Kano

RelatedPosts

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Masana harkokin lafiya sun yi tabbacin...

Marmari

Kayan Marmari 12 Da Ake Bukatar Yawaita Sha Lokacin Zafi

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Sau da yawa kuma in ji...

Gashi

Amfanin Gashi A Jikin Dan Adam (2)

by Muhammad
2 weeks ago
0

Cigaba daga ranar Talatar da ta gabata.   Gashin kai...

Next Post

Jami`an Kananan Hukumomin Jahar Yobe Sunyi Taron Tattaunawa Akan Cutar Foliyo A Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version