Muhammad Maitela" />

Gwamnatin Jihar Borno Ta Gina Gidaje 30, 000 Don Tsugunar Da Wadanda Rikici Ya Rutsa Da Su

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana kammala gyara wa tare da gina sabbin gidaje sama da 30,000, a sassa daban-daban a jihar- ciki har da yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa, wanda ya hada da rukunin gidaje guda 6, masu dauke da gidaje 2, 500 a cikin birnin Maiduguri.
Gwamnatin jihar ta bayyyana hakan ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Borno- Malam Isa Gusau. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kammala gina gidaje 11,000 a garin Bama, tare da karin sake gina wasu gidajen kimanin 7,000 a karamar hukumar Mobbar. A hannu guda kuma, gwamnati ta sake gyara gidajen da mayakan suka barnarnata a, kimanin 3,000 a karamar hukumar Mafa, sannan da wasu gidajen jama’a, 2,500 wadanda aka lalata a garin Damboa.
Isa Gusau ya kara da cewa, “baya ga wadannan kuma, gwamnatin Alhaji Kashim Shettima, ta hanyar ma’aikatar farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa a jihar Borno, ta sake gina wa tare da gyara gidaje 2,500 a karamar hukumar Gwoza da gidaje 2,000 a Konduga”.
“bugu da kari kuma, gwamnatin jihar ta kammala sake gina karin wasu gidajen jama’a, wadanda wannan lamarin ya shafa, kimanin 1,000 a karamar hukumar Nganzai da kuma aikin gama gina gidaje 432 a karamar hukumar Kaga”.
Malam Isa ya kara da cewa, lamarin bai tsaya nan ba; inda baya ga kammala gina gidajen, a kananan hukumomin, da suka hada da na garin Gamboru, ta karamar hukumar Ngala, gwamnatin kuma ta kammala gina sakatariyoyin kananan hukumomin, gidajen sarakuna da cibiyoyin yan-sanda da kotunan yankin, da matsalar ta shafa.

Exit mobile version