Gwamnatin Jihar Edo Na Shirin Bunkasa Harkar Noma

Daga A.A. Masagala,  Benin

Gwamnatin jihar Edo ta  shirya tsare-tsare da hanyoyi, ta yadda za a samu damar bundasa harkar noma a fadin jihar a yayin da ta nuna cewa yana daga shirinta na samarwa dubban matasa  ayyukan yi.

Kwamishinan sashin albarkatun noma na jihar Honarabul Monday Osagboro ya fadi hakan ne a wani taro da aka gudanar  a Odeguete da ke daramar hukumar Obia ta gabas.

Kwamishina Monday Osagboro ya ba al’umman wannan yankin tabbacin  cewa burin gwamnatinsu shi ne bundasa  harkar noma ta hanyar tallafawa manoma da kayan aiki irin na zamani domin su samu damar tafiyar da kome a cikin saudi kuma a cewar kwamishinan gwamnatinsu a shirye take ta cigaba da samarwa matasa ayyukan yi a cikin jihar.

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, wani mai fada a ji na yankin daramar hukumar Obia din Barrista  Julius Edebor  ya godewa wannan kwamishinan da ziyarar da ya kai ayankin inda yake cewa wannan ziyarar ta kwamishina abar alfahari ce, domin ya nuna irin yadda gwamnan jihar Godwin Obasike yke daunar cigaban al’umman yankin da jihar baki daya.

 

Exit mobile version