Lawal Umar Tilde" />

Gwamnatin Jihar Filato Ta Kasafta Kashe Naira Bilyan 133.8. A Shekara Ta 2021.

Gwamnatin Jihar Filato

Gwamnan jihar Filato Honarabul Simon Bako Lalong, ya mikawa ‘yan majalisar dokoki na jihar kasafin kudi na Naira Bilyan daya da talatin da uku da Naira Miliyan dari takwas (N133.8bn) da gwamnatin jihar ta kasafta za ta kashe a shekarar 2021.
A lokacin da gwamnan yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar a makon da ya gabata ya ce, kasafin kafin a gabatar da shi, sai da aka zauna da masana tattalin arzikin aka yi nazarin ainihin abinda jihar za ta iya samu a yanzu bisa la’akarin da halin matsi tattalin arziki da duniya ta shiga a sakamakon cutar Korona.

Haka kuma ya ce, kasafin kudin na Naira bilyan dari daya da talatin da uku, da Naira Miliyan dubu dari takwa da biu da dubu dari bakwai da dari bakwai da biyar, da dari hudu da hamsin da biwai, (N 133,482, 705,457.00) wanda aka yi wa lakabi da kasafin kudin karfafa tattalin arzikin jihar da inganta masana’antu, zai fi mai da hankali wajen tabbatar da tsaro da inganta zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar. Kasafin kudi na wannan shekara ya dara na shekarar da ta gabata da Naira Bilyan Goma da Naira Miliyan dari Biyar (N 10.5) idan a ka kwantanta da na Naira Bilyan dari daya da Ashirin da biu da Miliyan dari Takwas (bn 122.8)  da gwamnatin jihar ta gabatar a shekarar da
ta gabata wadanda akayi amfani dasu a wannan shekara  ta 2020.

Gwamnan ya ce, karuwar kudin ya biyo bayan karuwan samun kudaden shiga da gwamnatin take sa ran samun su. Gwamna Lalong, ya tabbatar wa al’ummar jihar nasarar samun kudade shiga masu yawa a bisa dalilin kwararrun ma’aikata da gwamnati mai ci yanzu a jihar ta dauka,  sannan sai ya bukaci al’ummar jihar da su kara ba su hadin kai da goyon baya don gwamnati ta samu nasarar aiwatar da ayyukanta cikin nasara.

Exit mobile version