Gwamnatin Jihar Gombe Na Bai Wa Fannin Noman Auduga  Mahimmanci - Kwamishina
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Jihar Gombe Na Bai Wa Fannin Noman Auduga  Mahimmanci – Kwamishina

byAbubakar Abba
2 years ago
Gombe

Gwamnatin  jihar Gombe ta bayyana cewa, ta na bai wa harkar noman Auduga muhimmanci, musamman domin ta kara bunkasa fannin a daukacin fadin jihar, samar da ayyukan yi ga ‘yan jihar,  kara habaka tattalin arzikin jihar da kuma kara bai wa manomanta kwarin guiwa.

Furuncin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Aikin Gona na Jihar, Muhammad Magaji Gettado a jawabinsa a lokacin want taro da aka gudanar a kwanan baya a jihar akan yadda za a kara bunkasa fannin, musamman a jihar.

  • Takaddamar Da Ta Kunno Kai Lokacin Tantance Ministocin Tinubu
  • Gwamna Dauda Ya Karbi ‘Yan Mata Hudu Da Suka Kwashe Watanin 7 A Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

A cewarsa, a baya manoman na Audugar a jihar sun funaci matsaloli, inda ya bayyana cewa, amma tuni gwamnatin jihar ta magance wadanan natsalolin, musamman ganin yadda ta samar wa manomanta kayan aikin noma na zamani da sauransu

Magaji ya kara da cewa, akwai kuma bukatar a ilimantar da manomata, musaman wajen samar masu da ingantacce Iri wanda hakan zai taimaka masu don su kara bunkasa noman na su na Audgar a jihar.

A cewarsa,”Gwamnatin Jihar ta na bai wa harkar noman auduga muhimmanci kasancewar ta fanni ne da ke kara bunkasa tattalin arziki. “

Shi kuwa a na sa jawabin a matsayin babban bako a wajen taron shugaban kungiyar manoman Auduga na kasa Alhaji Lawan Sani Matazu, ya bayyana cewa, a watannin da suka gabata, kungiyar ta kaddamar da shirin  habaka noman Auduga a jihar, wanda ya ce, waccan kaddamar kwaliya ta but ya kudin Subulu, musamman ganin cewa, fannin na kara bunkasa a jihar.

A cewarsa, jihar ta Gombe  kusan a daukacin fadin kasar nan, ita ce ke a gaba wajen noman auduga, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ci gaba da bai wa fannin mahimmanci domin jihar ta ci gaba da rike wannan kambun na ta.

” A watannin da suka gabata, kungiyar ta kaddamar da shirin  habaka noman Auduga a jihar, wanda ya ce, waccan kaddamar kwaliya ta but ya kudin Subulu, musamman ganin cewa, fannin na kara bunkasa a jihar.  “

Matazu, ya ce noman Auduga hanyar ci gaba ne ga matasa domin, fannin na samar da aikin yi da kuma kudin  shiga, musamman ga manoman da suka rungumi fannin ka’in da na’in.

Ya  buga misali da cewa, ingantacce Irin nomanta da Babban Bankin Nijeriya CBN, ya rabarwar da wasu manomanta ‘ya’yan kungiyar a jihar ta Gombe, hakan ya kara taimaka wa wajen kara bunkasa nomanta a jihar da kuma kasa baki daya.

“Ingantacce Irin nomanta da Babban Bankin Nijeriya CBN, ya rabarwar da wasu manomanta ‘ya’yan kungiyar a jihar ta Gombe, hakan ya kara taimaka wa wajen kara bunkasa nomanta a jihar da kuma kasa baki daya. “

Kazalika ya bayyana cewa,bashin, da bankin ya bai wa manomanta a jihar shi ma ya taimaka wajen bunkasa sana’ar su da kara samar wa da kansu da kudaden shiga.

Shugaban ya kuma yi kira ga manomanta da su tabbatar da suna shuka ingantacce irin na Audugar domin su dinga samun dimbin kudaden shiga da kuma samun amfani mai yawa idan sun yi girbi.

” Ina kira ga manomanta da su tabbatar da suna shuka ingantacce irin na Audugar domin su dinga samun dimbin kudaden shiga da kuma samun amfani mai yawa idan sun yi girbi. “

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 122 A Nijeriya -UNICEF

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 122 A Nijeriya -UNICEF

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version