Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Amince Da Biyan Masu Unguwanni

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da biyan albashi ga masu unguwanni 17,139, a cikin masarautu 34 da take da su na jihar, an yi hakan ne saboda su rika ba da ta su gudummawar wajen  allurar riga-kafi musamman wadda za ta taimaka wajen maganin kamuwa da munanan cututtuka. Kodayake ita jihar jihar Kaduna ba ta samu bullar wani al’amarin da ya shafi Polio tun shekarar 2012 lokacin da aka ba da sanarwa mai nuna cewar jihar ba tada wani al’amarin da ya shafi Polio ba.

Da yake jawabi ga manema labarai kwamishinan kananan Hukumomi na jihar, Farfesa Kabir Mato, kwamishinan lafiya da jin dadin jama’a Dokta Paul Dogo, shugabar Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Kaduna Dokta Hadiza Balarabe, sun  yi bayani a kan irin gudummawar da masu unguwanni suke badawa, wajen allurer rigakafi wadda akan yi lokaci zuwa lokaci, wanda yin hakan ne ya sa aka bada sanarwa jihar ta yi bankwana da cutar Polio.

Mato ya bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kasance Naira milyan 170 ko wane wata, saboda biyan ko wane mai unguwa albashin Naira dubu goma ko wane wata , a  matsayin albashi. Matsayin wani taimako domino ana jin dadain gudummawar da suke badawa, musamman lokacin ake yin allurar Polio.

Mato ya bayyana cewar lokacin mulkin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i, ya dade yana amfani da kukin jihar, da kuma taimako daga abokan harkar jihar masu ta kasance da ci gaba saboda maganin mutuwar mata masu juna biyu lokacin haihwa, da kuma kananan yara. Da kuma taimakawa wajen bunkasa asibitoci wauraren da ake kula da lafiyar al’umma, tun shekarar 2015 an dauki matakai na daukar muhimmanci alluran riga-kafi bada wasa ba, wajen da an tabbatar da je ko wane sako da kuma lungu na jihar, saboda aba yara abubuwan da suke so, domin kauce ma har sai an kai yin allurar rigakafi kamuwa da munanan cututtuka.

Kamar yadda kowa ya sani an sha yin su wadannan alluran riga-kafin, ana kuma ci gaba da yin sa saboda a kare kananan yara daga kamuwa daga cututtuka, gwamnan jihar Kaduna ya nuna yadda ya kamata a rika yi saboda ya kawo ‘ya’yan shi wajen allurar, wannan kuma ba domin komai ba sai saboda a jawo hankalin wasu iyaye suma , su yarda a yi ma ‘ya’yan nasu allurar riga-kafin.

Bugu da kari ita gwamnatin da kuma masu taimaka mata, ta dauki matakan da duk suka kamata a dauka, na tabbatar da na ci gaba da yin alluran riga-kafin, wannan ya nuna ke nan dukkan kayayyakin da ake bukata dangane da allurar rigakafi, ana dade da tanadarsu ko da kuwa shekara daya zasu yi.

Nasarorin da ka samu dangane da alluran riga-kafin abin ya samo asali ne, a kan irin gudummawar da masu unguwanni suke badawa, saboda sune suka fi kowa sanin wadanda suke zaune dasu, da suka hada da su yaran da kuma sauran wadanda ake bukata domin cim ma burin.

 

Exit mobile version