Connect with us

TATTAUNAWA

GWAMNATIN JIHAR KATSINA A BAKIN AIKI

Published

on

A

wannan watan na Satumba shekara ta 2018 ma, mun tattaro muku rahotanni daga jihar Katsina, na irin yadda gwamnatin jihar  kar kashin jagorancin, Mai Girma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ke gudanar da ayyukan jin  kai, tausayi da tallafawa rayuwar talakawa.

Kamar yadda gwamnatin ta gwamna Aminu Bello Masari ta yi al kawari a yayin ya kin neman za be, na cewa idan a ka za be shi zai tafiyar da gwamnatinsa ne a bu de, ta yadda talakawa za su ri ka sanin yadda a ke tafiyar da jihar. Haka kuwa ya kasance, domin a bu de a ke gudanar da duk wasu aikace – aikacen jihar.

 

Gwamnatin APC Za Ta Tsamar Da Al’umma Daga Talauci –Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masrai ya  kara bayar da tabbacin cewa gwamnatin Apc a fa din tarayyar Nijeriya da Jihar Katsina za ta ci gaba da gudanar da ayyuka don rage ra da din talauci ga al’umma.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wannan bayani ne a wurin taron  kaddamar da shirin bayar da tallafi ga al’umma a garin Rimi.

Gwamnan ya ce, gwamnati ba ta iya tabbatar da wanzuwar tsaro a cikin al’umma matu kar al’ummar na fama da talauci.

Ya yi bayanin cewa tsarin samar da tallafi na gwamnatin jam’iyyar APC yayi kama da irin tsarin da  kasashen larabawa da  kasashen da suka ci gaba suke amfani da shi wanda kuma ya taimaka wurin hana matasansu shiga harkokin fashi, sata da sauransu.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi shelar cewa shirin a nan gaba zai taimakawa mutane wurin sama musu ayyukan yi da horaswa, musamman ma matsan da ke  kasa da shekar 18, ta yadda shirin zai tallafa ba tare da dubi ga  bangaranci siyasa ko addini ba.

A jihar Katsina, Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta gamsar da jama’a cewa ta hanyar yin aiwatar da tsare-tsare kan ilimi, lafiya, noma da tsaro ake samun ci gaba. A yi su yadda ya dace ba tare da kawo siyasa a ciki ba.

Alhaji Aminu Bello Masari ya nemi matan da za su samu wannan tallafi da su yi amfani da shi wurin gudanar da  kananan sana’o’i don taimakawa kawunansu.

Ya ce, ta hanyar yin hakan ne za su samu damar tura ‘ya’yansu makarantu kuma a iya samun ilimin ‘ya’ya mata.

 

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Yi Ha din Gwiwa Don Bun kasa Kasuwancin Fitar Da Ri di

Bankin shigi da fici na Nijeriya da gwamnatin Jihar Katsina sun cimma yarjejeniyar yin ha din gwiwa domin bun kasa kasuwancin fitar da irin ri di. Lamarin da zai bun kasa harkar noman jihar.

A na sa ran Bankin zai sa hannu a kan  yarjejeniyar da gwamnatin Jihar Katsina wanda zai kai ga kafa kwamitin da zai gudanar da shirin.

Wannan shirin yana  daya daga cikin shirye-shiryen bankin a fa din tarayyar Nijeriya, wanda aka samar da shi don samar da wasu hanyoyin shiga ba tare da dogaro da  bangaren man fetur ba.

Babban Manajan Bankin na NE DIM, Malam Abba Bello ne ya bayyana wannan ha din gwiwa a lokacin wata ganawa da suka yi da gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari.

An yi wannan ganawar ne da zimmar tattauna hanyoyin samar da damammaki da kuma bun kasa harkar fitar da kayan gona daga Katsina zuwa kasuwannin duniya.

Bello ya sanar da Gwamna Masari cewa tuni dai an ware naira  biliyan  daya domin a bun kasa harkar fitar da kayan gona a jihohi 36 da ake da su a fa din Nijeriya ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa tsarin nasu, wanda yake tafiya kafa da da kafa da da shirin ‘One state, one product project’ wanda ke da zimmar inganta kayan gona a jihohi da taimakawa masu kasuwancin fitar da kayan zuwa wasu  kasashe.

Shugaban Bankin na NE DIM ya bayyana cewa duk da naira biliyan  daya ta yi ka dan wurin wannan aikin amma zuwa nan gaba za a fa da da lamarin.

Ya kuma  kara yin kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta taimaka wurin cimma muradin fitar da wannan iri na ri di zuwa wasu  kasashe, wanda yana  daya daga cikin abubuwan da aka fi nomawa a jihar kuma mutanen yankin Asiya ke matu kar bu katarsa.

A na shi bayanin, Gwamnan Jihar Katsina ya ce, wannan ha din gwiwa ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar k eta  ko karin samar da hanyoyin bun kasa harkar kasuwancin fita da kayan gona zuwa wasu  kasashe. Wanda kuma wannan zai taimaka wurin samar da ayyuka da bun kasar tattalin arziki a Jihar Katsina.

 Kananan Hukumomi Tara Za Su Samu Tallafin Miliyan 144 Daga UNICEF

Kimanin  kananan hukumomi tara ne za su samu tallafin naira miliyan 144 daga tallafin UNICEF, wanda za a basu domin farfa do da harkar ilimi a fa din jihar Katsina.

Kananan hukumomin kamar yadda UNICEF ta bayyana su ne, Kankiya, Safana, Kankara, Batsari, Baure, Mani, rimi, Sabuwa da faskari.

Mai kula da fannin ilimi na UNICEF a Jihar Katsina, Muntaka Mukhtar Muhammad ya bayyana haka a lokacin da yake  kaddamar da kwamitin sa ido kan ayyuka na  kungiyar wanda ya gudana a ofishin SUBEB na Jihar Katsina.

Ya bayyana cewa, makarantun firamare 95 da kuma makarantun allo na zamani ne za su samu wannan tallafi a jihar Katsina.

Ya ce; “UNICEF ta ware naira miliyan 144 inda kowacce makaranta za ta samu aikin da ya kai na kimanin naira miliyan 1.5. na yi matu kar jinjinawa  ko karin gwamnatin Jihar Katsina bisa  ko karin da ta ke yi a kan bun kasar ilimi” inji shi

Tun a farko, a na shi jawabin, Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Katsina, alhaji Lawal Buhari Daura ya yabawa irin goyon bayan da UNICEF ke ba makarantun firamare a jihar Katsina.

Ya ce, duk da cewa gwamnatin Jihar Katsina ta na matu kar  ko kari wurin ciyar da fannin ilimi gaba, ga kuma  kungiyoyi daban-daban na kawo nasu gudummawar.

 

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Mayar Da Ma’aikata 400 Bakin Aiki A  Kananan Hukumomi 34

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da batun mayar da ma’aikata sama da 400 bakin aikinsu a  kananan hukumomi 34.

Shugaban  Kungiyar Ma’aikatan  Kananan Hukumomi NULGE ta Jihar Katsina, Kwamared Aliyu Haruna Kankara ne ya bayyana haka yayin da yake yabawa matakin da gwamnatin ta  dauka na mayar da sub akin aikinsu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, Shugaban  Kungiyar ta NULGE, Kwamared Aliyu ya bayyana cewa wa danda abin ya shafa an kore su a aiki ne bisa sa hannun kwamitin da aka kafa don sa ido akan latti da rashin zuwa aikin ma’aikata a  kananan hukumomi 34 da ake da su a jihar.

Haka kuma shugaban ya bayyana cewa, wannan ya zama aya a tsakanin ma’aikatan  kananan hukumomi wa danda ba su son zuwa aiki a kan kari, ko masu fashi da gangan.

Haka kuma ya  kara da yabawa gwamna Masari bisa namijin  ko karin da yayi na dawo da sama da ma’aikata 2,000 a bakin aikinsu, wa danda gwamnatin da ya gada ta kora daga iki.

 

Tattara Bayani Daga Kamfanin

DANKAMA MEDIA CONCEPT, KATSINA

 Daukar Nauyin Bugawa:

GWAMNATIN JIHAR KATSINA

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: