Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Lashi Takobin Hana Al’umma Shiga Talauci

Published

on

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi alkawarin yin hadin gwiwa da cibiyoyin gwamnati da kuma bangarori masu kansu domin fitar da al’umma daga kangin talauci.

Mataimakin gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ofishinsa, ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da shirin bunkasa kanana da matsakaitan sana’o’i a karkashin hukumar samar da ayyukan yi ta kasa a dakin taro na tsohon gidan gwamnati.
Kamar yadda yace, shirin sananne ne wanda ke karkashin hukumar samar da ayyukan yi ta kasa da ke da nufin taimakama masu kanana da matsakaitan sana’o’i don bunkasa kasuwancinsu.
Mataimakin gwamnan yace karkashin shirin an raba kudade ga mutanen da su ka fito daga kananan hukumomi 34 na jihar nana.
Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana cewa, wadanda su ka amfana da shirin sun hada da matasa da masu bukata ta musamman da wadanda mazajensu su ka rasu da kuma gajiyayyu inda a ka ba kowannensu Naira 10,000.
Ya bayyana cewa rabon kudin ya zo dai-dai lokacin da annobar cutar corona ta shafi tattalin arzikin duniya.
Mataimakin gwamnan yace tun lokacin da aka fara shirin taimakama ‘yan kasuwa, mutane sama da dubu uku su ka amfana da shirin a jihar Katsina.
A tsokacinsa, shugaban hukumar saka hannun jari ta Katsina Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya shawarci matasa dasu tsunduma cikin sana’o’I domin zama masu dogaro da kansu.
Tunda farko a jawabinsa na maraba, jami’in hukumar samar da ayyukan yi ta kasa a jihar Katsina, Yarima Sa’adu yace shirin tallafama ‘yan kasuwar nada nufin taimakama kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa domin bunkasa tattalin arziki daga tushe.
Ya ce, mutane dubu daya su ka amfana da shirin rabon kudin a kananan hukumomi 34 da ke jihar Katsina.
Advertisement

labarai