Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Jihar Kebbi Da Kamfanin MECA Sun Kulla Yarjejeniya Kan Kula Da Taraktocin Noma 100

Published

on

Gwamnatin Jihar Kebbi da Kamfanin samar da kayan aikin noma na Afirka (MECA), sun kulla   yarjejeniyar  don kula da  taraktocin noma guda dari mallakar gwamnatin jihar.
Sun rattaba hannun ne a karshin ahiein aikin noma na  gwamnatin jihar ta Kebbi.
Kwamishinan  ma’aikatar aikin noma da albarkatu na jihar Barista Attahiru Maccido ne ya sanya  hannu a madadin gwamnatin Jihar, yayin da Daraktan Kamfanin dake a Nijeriya, Iliya Gashinbaki ya sanya hannu a madadin kamfanin.
Da yake jawabi a wurin bikin rabbata hannun, kwamishinan Maccido ya ce, Gwamnan jihar Alhaji Atiku Bagudu ya amince da shigar da ma’aikatar noma, tare da bayar da shawarar daukar wannan tsari da MECA, domin kula da taraktocin noman guda   dari da gwamnatin jihar ta saya.
Ya kara da cewa, Gwamnatin Jihar ta Kebbi, zabo kamfanin ne, sabodada ya cancanta kuma ya kware don tabbatar da nasarar shirin. Kwamishinan ya ci gaba da cewa, daga cikin taraktocin 50,  za a tura su zuwa yankuna hudu  na gonakan dake a jihar a karkashin hukumar kula da aikin noma da raya karkara ta Kebbi wato.(KARDA) da.suka hada da  cikin Argungu, Bunza, Zuru da Yauri a cikin jihar ta kamfanin kuma za a samu, musamman
don hayar ga kananan manoman dake a jihar ta Kebbi.
Ya ce za a baiwa sauran taraktocin noman guda 50 guda  da suka rage wa manyan manoma bisa biyan kudin ajiya, wadanda kamfanin zai kuma sarrafa su.
Tun da farko, a nasa jawabin a wurin bikin na rattaba hannu, Babban Sakatare a Ma’aikatar aikin noma da albarkatun na jihar Mista Joel Aiki, ya bayyana sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayin wani abin yabawa, inda ya ce, hakan ya nuna a zahiri kan himma da kuma kwazon gwamnatin jihar wajen ciyar da jihar gaba bisa mutunta fannin aikin gona a jihar.
Ya yi nuni da cewa, wannan, wani bangare na yarjejeniyar ya hada da tsaro, tabbatarwa da kuma daukacin rukunin taraktocin noman guda  100 da gwamnatin jihar ta samar, ban da yawan kayan sarrafa kayan gona don tallafawa aikin gona wanda tuni aka rarraba.
Ya bada tabbacin hakan, Gwamnatin Jihar Kebbi ta dukufa wajen bunkasa harkar noma a jihar, don ciyar da kasar nan gaba, inda ya kara da cewa, aiki ya kuma nuna cewa, injin aikin gona zai inganta samar da aiki, da rage yajin aiki da aiki tukuru.
Babban Sakataren ya kuma bayar da tabbacin cewa, an zabo kamfanin na  MECA ne, saboda sun cika dukkan ka’idodin da ake bukata, a fagen fasaha da kuma kudi, don fito da canjin kwangilar.
Shima a nasa jawabin a wurin bikin na rabbata hannun, Daraktan Kasuwancin kasa na kamfanin na  MECA, Iliya Gashinbaki, ya bayyana farin cikin sa game da ci gaban, inda yana bayyana hakan a matsayin wata muhimmiyar nasara da gwamnan jihar Kebbi ta gabatar a kokarin ta na ci gaba da kasancewa jihar a matsayin babbar cibiyar bunkasa harkar noma a Nijeriya, musamman noman shinkafa.
Ya ce, taraktocin noman guda 100 zasu bayar da gudummawa wajen bunkasa noman kadada 200,000 a shekara, inda ya kara da cewa, idan aka sanyawa wannan zuwa shiyyoyi hudu na aikin gona a jihar, hakan zai samar da abinci da.dama a cikin jihar ta Kebbi.
Ya ce, matasa a jihar na da damar da za su sami horo kamar yadda injiniyoyi, Mataimakin Kamfanin kera taraktocin noma da kuma Fasaha.

Ya danganta  kokarin gwamnan Kebbi wajen amincewa da yarjejeniyar ba wai kawai a zahiri ba ne lokacin da ake fama da cutar ta COVID-19, sai dai wani yunkuri ne na magance matsalar rashin aikin yi a jihar Kebbi.
Ya ce, ina so in tabbatar wa gwamna da jama’ar jihar Kebbi cewa MECA ya yi hakan a jihohi da dama, mun aiwatar da aikin noma na  Fadamas a fadin jihohi 14 na Nijeriya, inda yace, mun kasance a jihar Kano, jihohin Neja kuma yanzu haka a jihar Kebbi.
Ya sanar da cewa, abinda yafi jan hankali shine, tunda cutar COVID -19 ta fara, wannan shine matakin farko da aka fara bayarwa don magance matsalar abinci a Nijeriya.
A karshe,  ya yi kira ga sauran Gwamnonin da su yi koyi da Gwamnan Kebbi wajen bunkasa fannin aikin noma a jihohin su don su kara wadatar da jihohin su da abinci mai yawa harda kasa baki daya.
Advertisement

labarai