Umar Faruk" />

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Biya Naira Miliyan 154 Ga KEDCO Don Karfafa Wutar Lantarki

Gwmantin jihar kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ta biya Naira Miliyan dari da hamsi da hudu ga hukumar Samar da wutar Lantarki ta Kaduna reshin ofishinta na jihar ta kebbi don su samar da wutar Lantarki awa ashirin da hudu a duk fadin jihar ta kebbi.
Bayanin hakan ne na kunshe a wata takardar da sakataren watsa Labarai na fadar gidan gwamnatin jihar da yasan yawa hannu Alhaji Abubakar Mu’azu Dakingari inda ya bayyana cewar” Kwamishinan Ruwa da wutar Lantarki na jihar, Alhaji Nura Usman Kangiwa ne ya bayyana hakan a jiya a Birnin-kebbi”.
Haka Kuma Kwamishina Nura Kangiwa ya kara da cewar gwamnatin jihar kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu saboda da sanin irin muhimmancin wutar Lantarki ga cigaban tattalin arziki mutanen jihar da kuma kasar Najeriya baki daya yasan gwamnatin tabbatar da cewar an samar da tsayayar wutar Lantarki ga jama’ar jihar ta kebbi don cigaban tattalin arziki mutane a jihar.
Har ilayau yace” gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu zata cigaba da tabbatar da cewar ta taimakawa hukumar samar da wutar Lantarki da tallafin kudi don bunkasa kudaden shiga na hukumar da kuma tabbatar da cewar sun gudanar da ayyukkansu ga jama’ar jihar ta kebbi da kuma samar da wutar Lantarki awa ashirin da hudu ga mutanen jihar.
Bugu da kari Kwamishinan ya shawarci jama’ar jihar da su tabbatar da cewar suna biyan kudaden wutar Lantarki akan kari. Hakazalika yace” a kwanan gwamnatin jihar ta kebbi ta sanya na’urar bada hasken wutar Lantarki watau Transformers gudu arbi’in a wasu yakunan kananan hukumomin jihar don tabbatar da sun samu wutar Lantarki wadatatta a garuruwansu.
Haka Kuma an sayo na’urorin transformers guda Tamanin domin su kasance a cikin wucin gadi da kuma tabbatar da cewar duk yakin da ke fama da matsalar na’urar bada hasken wutar Lantarki an sabunta musu wata.

Exit mobile version