Gwamnatin Jihar Yobe Tana Da Ingantaccen Tsarin Bunƙasa Noma -Kwamishinan noma

Baya ga ingantaccen tsarin da gwamnatin Jihar Yobe take da shi wajen bai wa manoman Jihar ƙwarin gwiwar aiwatar da ayyukan noman damina da na rani ta hanyar samar da kayan noma na zamani bisa kan kari. Haka zalika kuma, Gwamnatin Jihar ta ɓullo da waɗansu sabbin tsare-tsare da dabarun bunƙasa noman rani domin ganin tattalin arzikin Jihar ya haɓɓaka kuma ya bunƙasa sannan da samarwa matasa ayyukan yi, yayin da a wannan karon ta nemo wasu shirye-shiryen noman rani ta hanyar ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da ƙasar Chana domin koyawa manoman Jihar sabbin hanyoyin noman rani a Jihar. Gwamnatin ta bayyana cewa matuƙar manoman Jihar suka rungumi wannan sabon tsari, to kwalliya za ta biya kuɗin sabulu wajen samun wadatar abinci.

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Ta ce wannan tsarin ya zo ne bayan wani dogon nazarin da ta yi dangane da yanayin albarkatun muhalli da fadamun da Allah ya azurta yankin da su, sannan kuma da la’akari da cewa mafi yawan al’ummar Jihar sun dogara ga ayyukan noma a matsayin hanyar samun kuɗin shiga da abinci sannan uwa uba kuma ta yi nazarin cewa muddin lokacin damana ya wuce sai matasa da talakawa su tsiri zaman kashe wando, yanayin da ta ce ya yi kama da ƙishirwa na neman kashe mai dono. Ta yi ƙarin haske dangane da wannan sabon tsari na noman rani wanda manoman China suka zo su koyawa matasan sabbin dabarun noman wanda ta bayyana cewa ya kai faɗin murabba’in hekta ɗari biyar (500) a cikin ƙananan hukumomi huɗu dake Jihar ta Yobe.

Bisa ga wannan ne dama wasu shirye-shirye da Gwamnatin Jihar Yobe take da su wajen bunƙasar noma da manoma Mujallar Manoma ta zanta da Kwamishinan ayyukan noma da muhalli na Jihar, wato Hon. Injiniya Mustafa Gakerema a ofishinsa dake Damaturu Babban Birnin Jihar inda ya fara da fayyace zare da abawa tare da bayyana shirye-shirye da ƙudurce-ƙudurcen ma’ikatar noman da cewa”bayan tunani da Gwamnatin Jihar Yobe ta yi dangane da yadda matasan mu da ma sauran al’ummar wannan Jiha ta mu suke kasancewa bayan kammala noman damana, inda wasu ke cigaba da zaman kashe wando, bayan kuma ga shi Allah ya azurta mu da ƙasar noma mai kyau, musamman yadda muke da kogin Kuma-Dugu shi ne Maigirma Gwamna, Alhaji Ibrahim Gaidam ya ƙulla wata yarjejeniya ta haɓaka noman rani da ƙasar China, inda suka zo suka koyawa matasan mu sabbin dabarun noman rani”.

Haka zalika kuma Kwamishinan ya ƙara da cewa “wannan aiki na noman rani ya ƙumshi murabba’in hekta ɗari biyar (500) ne a cikin ƙananan Hukumomi huɗu; akwai Fadamar Nguru inda muke da hekta ɗari biyu (200) sai kuma a ƙauyen Boloram dake cikin ƙaramar Hukumar Gaidam mai faɗin hekta ɗari biyu (200) shi ma, sannan kuma da Garin-Gada dake ƙaramar Hukumar Yunusari mai hekta kusan hamsin (50) sai na ƙarshe shi ne ƙauyen Jumbam dake Tarmowa shi ma kusan hekta hamsin (50). Insha-Allah mun tsara za a noma alkama da shinkafa da kuma kayan lambu a cikin waɗannan gonakai da na lissafa maka, sannan da yake dama can waɗannan muhallan mallakar Gwamnati ne kuma wasu har an kammala samar da madatsun ruwa a cikinsu misali a Nguru sannan kuma an kawo injuna da na’urori da sauran kayan aiki”. Inji Kwamishinan.

“Haka kuma zan iya bayyana maka cewa, wannan aikin zai ci kuɗi sama da naira miliyan ɗari biyar (N500,000,000) kuma Gwamnatin Jihar Yobe ta fito da wannan shiri ne domin ganin cewa matasanmu sun samu aikin yi wanda za su dogara da shi don ta rage zaman kashe wando sannan da bunƙasa tattalin arzikin al’ummar mu don rage dogaro ga Gwamnati. Sannan kuma an raba waɗannan gonakin ga matasa kuma shirin zai cigaba da gudana; idan an koyawa waɗannan matasan sai a sake ɗibar wasu su ma haka abin zai cigaba. Sannan gwamnati kuma ta ba su ƙwarin gwiwa wajen ƙarfafasu. Kuma Insha-Allah, muna sa ran hakan zai taimaka gaya wajen haɓakar tattalin arzikin wannan Jiha”. Ya nanata.

“Haka zalika kuma, mun baiwa manomanmu na damina da lambu waɗanda suka fito daga  yankunan da matsalar Boko Haram ta sa suka bar muhallansu kuma waɗanda suka kwashe sama da shekara uku ba su noma ko bunga ba tallafi, shirin tallafi ne na musamman tsakanin Gwamanatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Bayar da Agajin Gaugawa ta ƙasa (NEMA) da hukumar agaji ta (SEMA ) ƙarƙashin Jihar Yobe wajen ba su tallafi na musamman dangane da kayan noma don farfaɗowa daga halin da suka shiga, amma kuma wannan ba yana nufin ba a baiwa sauran manoman kulawa ba, su ma sun samu nasu kason domin baki ɗayan su manoma ne dake Jihar Yobe kuma kowa na cin gajiyar shirin Gwamnatin Jiha na baiwa manoma tallafi kamar yadda aka saba kowace shekara”. Ya sha alwashi.

Injiniya Mustafa Gajerema ya yaba da namijin ƙoƙari da goyon baya da Ma’aikatar Ayyukan Noma da Muhalli ke samu daga Gwamnatin Jihar Yobe, inda ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shi ne sirrin nasarorin da ma’aikatar ke samu. Yayin da kuma ya ɗara tunatar da al’ummar Jihar Yobe dama ƙasa baki ɗaya da cewa, ayyukan noma su ne ginshiƙi kuma ƙashin bayan cigaban kowace ƙasa a duniya inda ya ce”babban saƙon tunatarwa da zan yi ga jama’ar Jihar Yobe shi ne yanzu lokaci ya yi da za mu rungumi ayyukan noma gadan-gadan, saboda amfanin kan mu da ƙasar mu baki ɗaya, ta wannan ne za mu samu abin da za mu iya dogara da shi kuma mu rage tsammani daga Gwamnati saboda ba zai yi wu a ce Gwamnati ce za ta yi mana komai ba kuma idan mun lura da manyan ƙasashe masu faɗa-a-ji a duniya irin Amurka da China duk sun dogara ne a kan noma kuma ga shi nan sun cigaba fiye da kowace ƙasa a duniya”.

“Allah ya horewa wannan Jiha ta mu ta Yobe yanayi da kuma dazuzzukan noma baya ga shimfiɗaɗɗiyar fadamar da kogin Koma-Dugu ya ratsa a ciki, sannan kuma za mu iya noma kusan kowane nau’in kayan abinci ko lambu. Sannan ban yi maka zancen kyakkyawan yanayin kiwata dabbobi ƙanana da manya ba kuma wadda jihohi da dama da mu suka dogara a nama da madara ko fatun dabbobi. Wannan ya ishe mu abin alfahari da tinƙaho a tsakankanin wasu ɓangarori a ƙasar nan. Saboda wannan Gwamnatin Jihar Yobe ba ta yin ƙasa a gwiwa wajen tanadin ɗiyaucinta kuma abin alfahari wanda kuma shi ne ƙashin bayan cigaban al’ummar ta da haɓakar tattalin arzikinta. Sannan ma’aikatar gona da muhalli a Jihar Yobe tana yin aiki tuƙuru wajen dawo da martabar noma a zukatan al’ummar Jihar don yin gogayya da kowace Jiha a ƙasar nan”. Ya bayyana.

Bugu da ƙari kuma, bisa ga wannan ne gwamnan jihar Yobe Alh Ibrahim Gaidam ya jaddada cewa jihar ta kama turbar kasancewa a sahun gaba wajen noma kayan amfanin gona, bisa wannan ingantaccen shiri na farfaɗo da ayyukan noman rani a yankunan jihar. Ya bayyana hakan ne a sa’ilin ziyarar gani da ido dangane da filayen noman da gwamnatin ta ware domin bunƙasa noman shinkafa, alkama, masara da makamantan su a waɗannan filayen noma dake yankunan ƙananan hukumomin Nguru, Gaidam da Bursari dake jihar.

Gwamna Gaidam ya sha alwashin cewa gwamnatin sa ta ƙuduri aniyar tallafawa manoman jihar Yobe domin cimma muradun da suke dashi na bunƙasa jihar da wadataccen abinci dama ƙasa baki ɗaya. Ya nanata cewa, babu gudu ba ja da baya wajen aiwatar da manufofin da wannan sabon tsarin ya ƙunsa, “saboda mun yi imanin muddin wannan shirin ya ɗore, to ko shakka babu, nan gaba kaɗan jihar Yobe zata jagoranci sauran ɓangarorin ƙasar nan a fagen noma kayan abinci da suka ƙumshi shinkafa, alkama da masara da sauran su, ta fuskar fitar dasu zuwa wasu yankuna dama ƙasashen waje”. Gaidam

 

Exit mobile version