Gwamnatin Jihar Yobe Za Ta Kashewa N795m A Kan Ilimi Da Kiwon Lafiya

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana ware kuɗi naira miliyan 795,083,650 wajen sayo na’urori tare da kayan aiki na zamani a manyan asibitocin jihar guda uku waɗanda ta sake faɗaɗa da bunƙasa su da ke Gashu’a da Potiskum da kuma Gaidam; yayin da asibitocin zasu laƙume naira miliyan 679 da ɗoriya daga wannan adadin.

Bugu da ƙari kuma, gwamnatin zata sayo tare da sanya kayan gwaje-gwajen kimiyya a ɗakunan binciken wasu manyan makarantun sakandiren jihar guda biyar da ta sake ginawa a GSS Fika, Nangere, Gwio-Kura da Yunusari, Nguru a jihar, yayin da kuma za a kashe naira miliyan 97 da ɗigo bakwai a aikin.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan yaɗa labara, da al’adu a jihar Yobe, Alhaji Mala Musti, ga manema labarai sakamakon zaman majalisar zartarwar jihar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam. Kwamishinan ya fara da bayyana cewa a cikin watan Yunin 2016 ne, gwamnatin jihar ta ware naira biliyan 1.8, domin sake gina manyan asibitocin jihar guda uku.

“A yau kuma, gwamnatin jihar ya amince da ware naira miliyan 679 da yan kai wajen sayo tare da girka na’urori da sauran kayan aiki na zamani a manyan asibitocin mu guda uku.” Mala Musti.

Kwamishinan ya sake tunatar da cewa, wannan mataki wanda gwamnatin Yobe ta ɗauka yana da dangantaka da ƙoƙarin Alhaji Ibrahim Gaidam wajen kyautata sha’anin kiwon lafiyar al’ummar jihar baki ɗaya.

Alhaji Mala ya ƙara da cewa” har wa yau gwamnatin Yobe ta amince da kashe naira miliyan 97, 703, 650 wajen cefano kayan gwaje-gwajen kimiyya a ɗakunan bincike da sauran kayan aiki a manyan makarantun sakandiri da jihar ta kammala gwarawa guda biyar”.

A wani batu na daban kuma, Gwamna Ibrahim Gaidam ya ƙara baiwa ɗaliban jihar ɗaliban jihar tabbacin ci gaba da basu tallafin karatu a cikin kowanme mataki na manyan cibiyoyin karatu a ciki da wajen ƙasar nan.

Gwamnan wanda ya yi ƙarin hasken ne kafin gudanar da zaman majalisasr kuma a daidai lokacin da kwamishina mai kula da sha’anin ilimin jihar, Alhaji Muhammad Lamin sa’ilin da yake miƙa masa lambar yabo wadda daɗaɗɗiyar ƙungiyar ɗalibai ƙasa reshen jihar (National Union of Yobe State Students) bisa ƙoƙarin da yake na bunƙasa sha’anin ilimin jihar.

Wanda a ƙarshe Gaidam ya nanata cewa gwamnatin sa zata ci gaba maida hankalin ta wajen biyan ɗalibai yan asalin jihar tallafin karatu waɗanda ke karatu a matakai daban daban kuma cikin lokaci.

 

 

Exit mobile version