Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

Zamfara

Daga Hussaini Yero,

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da rahotan rundunar ‘yan sanda na kame wasu jami’an tsaro bakwai da ke da hannu a taimakawa ayyukan ta’addanci a fadin jihar.

Kwamishina yada labarai na jihar  Zamfara, Honarabul Ibrahim Muhammad Dosara  ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gabata a ofishinsa da ke Gusau.

A cewarsa, wadanda ake zargin tuni aka yi musu tambayoyi kuma sun amsa laifukansu, suna yin zagon kasa wajan yakin da ‘yan bindiga, ta hanyar musayar bayanan sirri na sojoji, da samar da makamai da alburusai da kayan sojoji da sauran kayan aiki ga ‘yan bindigar don hana jaruman sojojin mu fatattakar ‘yan ta’addan. Tuni aka mika wadanda ake zargin ga hukumomin tsaron da suka dace don ci gaba da daukar matakan da suka dace a kan wadanda ake zargin.

Kuma an kama wanda ake zargin da harsasai guda  20 da bindiga a daidai lokacin da zai mika wa mai siyan bindiga Kabiru Bashiru na kauyen Maniya, wanda ake zargi da aikata fashi da makami.  Ya sa yi bindigar ce a kan Naira N100,000.00 .

“Wanda ake zargi na biyu, daga Sakkwato ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda da ke ba da kayan sojoji da kayan aiki ga wadanda ake zargin ‘yan fashi ne da harsashi na soja guda tara da riguna hudu na soja da katin ATM na banki guda biyu da aidikat na sojojin Nijeriya guda daya da wayar Samsun. In ji Kwamishina.

Kwamishina ya kara da cewa, a wani kokarin makamancin wannan, a ranar 1 ga Afirilu, 2021, wata tawagar ‘yan sanda da ke aiki a sashin manyan laifuka (SCU), yayin da suke aiki da bayanan sirri sun damke wasu mutum biyu da ake zargi daga karamar hukumar Zurmi da Shinkafi da ake zargin suna bai wa ‘yan bindiga, bindigogi da kayan sojoji daga Legas.

Kuma  a ranar 31 ga Maris, 2021, tawagar ‘yan sanda, a kan sintiri hanyar Wanke-Dansadau sun sake cafke wani wanda ake zargi daga yankin Rukuja na karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina.  A yayin gudanar da bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya fito ne daga daya daga cikin maboyar dajin Dansadau.  A yayin binciken ta wayar salula an gano hoton wanda ake zargin rike da bindiga Ak-47 da wasu manyan makamai na sa.

Mutum na biyar da ake zargi daga kauyen Kamarawa ta Karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato wanda likita ne aka samu nasarar cafke shi da zargi suna ba da kayan sojoji ga wadanda ake zargin ‘yan fashi da makami ne a cikin karamar hukumar Shinkafi.

“An kuma cafke wani wanda ake zargi a ranar 4 ga Afrilu, 2021 ta hanyar rundunar ‘yan sanda da ke aiki a sashin yaki da ta’addanci (CTU Base 18 Gusau) da mallakar bindigogi guda 2 da aka kera a cikin gida da harsasai masu rai guda 12, gungun laya da kudi kimanin Naira 523,000.00  .

A kan haka ne  gwamnatin jihar Zamfara ke kira ga shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Nijeriya da ya cika alkawarin da ya yi na tura sojoji 6,000 zuwa jihar don fatattakar  ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummomi wannan jihar tamu.

Gwamnatin jiha na kira ga hukumomin soja da su sanya ido sosai tare da sa ido kan ayyukan soji don tabbatar da hadin kai da tasirin yaki da ‘yan ta’adda.

A kan haka gwamnatin jihar Zamfara ke kira ga mutane da su rika samar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro da ke aiki a jihar don dawo da martabar Zamfara a idan duniya.

Exit mobile version