Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Kayan Aiki Ga Cibiyoyin Kiwon Lafiya 290
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Kayan Aiki Ga Cibiyoyin Kiwon Lafiya 290

bySulaiman
2 years ago
Cibiyoyin Kiwon Lafiya

Gwamna Uba Sani ya nuna farin cikinshi yayin da yake kaddamar da fara rabon sabbin kayan aiki na fasaha da aka siyo don inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (PHCs) guda 290 a jihar Kaduna. 

Gwamnan ya bayyana cewa,  hakan na cikin alkawuran da suka dauka na farfadowa da inganta ayyukan cibiyoyin Kula da Lafiya na matakin Farko don inganta harkokin lafiya ga al’ummar jihar Kaduna.

  • Gwamnatin Kaduna Ta Yi Murnar Sake Dawo Da Aikin Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya

“Bukatarmu a bangaren kiwon lafiya a matakin farko, ba wai raba kayan aiki ba ne kadai, za mu inganta fasahar ma’aikatan ta hanyar horarwa ta yadda za su yi fice a fanninsu, su bada ingantacciyar Kula ga marasa lafiya.

“Mun bada fifikon kulawa ga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko fiye da sauran, sabida su ne ke cikin Unguwanni 255 da ake da su a fadin jihar kuma su suke fara yaki da cututtuka da ke damun jama’a, don haka, in sun inganta, cibiyoyin kiwon lafiya matsakaita da manya za su samu saukin cunkoson jama’a.” inji Uba Sani

Cibiyoyin kiwon lafiya

Gwamna Uba Sani ya yaba wa Hukumar Kula da Kayayyakin Kiwon Lafiya ta Jihar Kaduna (KADHSMA) da Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kaduna (KSPHCB) da suka yi aiki ka-fada-ka-fada don ganin an kaddamar da fara raba kayayyakin don ci gaban al’ummar jihar.

“Abun godiya da jin dadi ne a gare ni yau, ganin na kaddamar fara rabon kayayyakin fasaha ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 290 da aka inganta a jihar Kaduna. Ina godiya a gareku.” Inji Gwamna Uba

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Har Yanzu Ina Jam'iyyar PDP, Amma Ina Aiki Da Gwamnatin APC —Wike

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version