Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El- rufai, a cikin shirinta na raya karkara da al’umma ta kaddamar da hanya mai tsawon kilo mita goma 12 wadda ta tashi daga Barwa ta shiga Zakada zuwa Bandi Amawa da ke Karamar Hukumar Kauru.
A Jawabinta yayin kaddamar da hanyar, Kwamishinar ma’aikatar raya karkara da al’umma ta jihar Hajiya Balaraba ta ce, wannan hanyar ita ce ta farko da ma’aikatarta ta fara kaddamarwa a cikin shekara daya da su kayi a ofis, Ta bakinta, “Hakika yau ranar farin ciki ne a gare ni kasancewar wannan hanyar ita ce irin ta na farko da ma’aikatarnmu za ta fara kaddamarwa a cikin shekara daya da mukayi a ofis. Haka kuma yau ranar farin ciki ne a gare ni, domin ta kassance ranar da muka cika alkawarin da gwamnatin Malam Nasiru Ahmed El-rufai ta dauka na inganta rayuwar al’ ummar karkara.”
Hajiya Balaraba ta ci gaba da cewa, hanyar mai tsawon kilo mita goma sha biyu wacce aka yi ta a kan kudi naira miliyan dari da casa’in da bakwai, daya ce daga cikin hanyoyi tara da ma’aikatar ta yi wanda za ta kaddamar da sauran nan ba da dadewa ba.
Ta ci gaba da cewa, “Gwamna ya fahimci cewa mafi yawancin mutanen jihar suna zaune ne a yankunan karkara, don haka ne ya mayar da hankalinsa wajen wadata su da hanyoyi, da kuma gyara asibitoci, makarantu, samar da wutar lantarki da ruwan sha mai tsabta. An sake dawo da ma’aikatar raya karkara da jin dadin al’umma ta wannan jihar a shekarar da ta gabata don tabbatar da an kawar da talauci, kuma al ummar karkara sun zama masu wadata da mutunci, don haka yin hanyoyi yakan saukaka fitowa da amfanin gona, karfafa kasuwanci, sada zumunci, da sauran harkokin rayuwa na yau da kullum kamar zuwa makarantu da asibitoci a cikin sauki”.
Bugu da kari, Hajiya Balaraba ta ce, Gwamnatin Malam Nasiru ta kafa kwamiti mai karfi domin duba duk muhimman abubuwan bukatun da jama’ar Karamar Hukumar Kauru ke da su don basu tallafin gaggawa.
A karshe, ta shawarce su da su yi kokarin kafa kugiyoyin ayyukan gayya domin ta haka ne kadai za su samu damar hadin kan da zai ba su damar cin moriyar dimokuradiyyan da muke ciki.
A jawabinsa na godiya, Aliyu Dahiru wanda shi ne Sarkin Garin Zakada, ya jinjina wa gwamnatin Malam Nasiru Elrufai bisa hanyar da ta samar musu. A cewarsa, “Mu kadai muka san wahalar da muke sha idan za mu shiga garuruwan da muke makwabtaka da su, amma yanzu an share mana hawaye, sai dai muna kara rokon mai girma gwamna da ya zo ya yi mana kwalta domin mu dade muna cin moriyar hanyar, sannan kuma muna baukatar a kara turo mana da abubuwan more rayuwa”.