Abubakar Abba" />

Gwamnatin Kano Na Dab Da Kammala Aikin Lantarki Na Tiga

Aikin samar da wutar na Megawat 10 na Wutar lantarki ta Tiga a yanzu ya kai kaso 90 cikin dari wajen kammala.

ji Injiniya Balarabe Shehu, daya daga cikin injiniyoyi masu kula da aikin ne ya sanar da hakan a Kano.

An dai faro aikin ne tun a lokacin tsohuwar gwamnatin tsohon gwamnan jihar , Inda yanzu aikin an kusan kammala shi.

Mista Shehu, wanda shi ne Shugaban Kamfanin MBS Engineering, ya bayyana haka lokacin da Gwamna Ganduje ya kai ziyarar duba aikin a Tiga.

Ya ce,“Mun yi farin ciki da muka fahimci cewa wannan gwamnatin tana ci gaba da yin aikin da gaske da jajircewa.”

Ya kara da cewa, bangarorin aiki da ake kura a turance, Control Room da Power Houses, da sauran su an kammala su 100 bisa dari. Muna fata ba zai ɗauke mu wata 2 ba zuwa 3 mu kaddamar da aikin, inda ya yi nuni da cewa, abinda ma zai sa aikin ya dauki wata biyu ko uku kafin a kammala shi ne shi ne akwai wasu abubuwa, musamman Dam din Tiga da sai jihar ta nemi izini da cike-ciken takardu daga Gwamnatin Tarayya, ya kara da haka.

A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya tabbatar da shirin gwamnatinsa na neman izini daga Gwamnatin Tarayya ya ce, muna kan tattaunawa da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta kasa, inda a saboda haka, kwanan nan wannan aiki zai kammala.

Ya ce, idan aka kammala aikin, zai kula da bukatun bangaren masana’antu a jihar.

A cewar sa, jihar mu za ta dawo zuwa karfin masana’antunta kuma wannan Megawat 10, kamar yadda muka ambata zai kula da masana’antunmu da fitilun kan titi a cikin birni.

Ya kara bayyana cewa ana yin irin wannan aiki a Dam din Challawa. Ya ce, bukatarmu ita ce mu tabbatar da cewa an warware matsalar wutar lantarki, kuma zuba jari zai habaka a jihar nan.

Ya ce, a saukake, muna samar da kyakkyawan yanayin da kasuwanci zai farfado da sauran kananan sana’o’i ma za su farfado. Kuma zai taimaka gaya wajen magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin al’ummarmu.

Exit mobile version