Gwamnatin Kano Na Daukar Matakan Kauda Yawaitar Mutuwar Mata Masu Ciki Da Kananan Yara

Likitoci

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

 

Gwamnatin jihar Kano za ta jaddada kokarinta domin kauda matsalar mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki a kokarin kauda matsalar.

Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar lafiya, Hadiza Mustapha Namadi ta raba wa manema labarai.

Dokta Aminu Ibrahim ya ce, taron na sanin makamar aiki ne don ilmantarwa da amfanan ma’aikatan lafiya da da samun hadin kan sauran masu ruwa da tsaki wajen damun nasarar magance mutuwar mata masu ciki da yara kanana.

Kwamishinan lafiya lafiyan na Kano ya ce, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta zo da muhimman tsare-tsare domin ganin an rage mutuwar mata masu ciki da yara.

Dokta Aminu Tsanyawa ya jaddada cewa Gwamnatin Ganduje a shirye take samar da wadatattun kayan aiki masu inganci don anfanar al’ummar Kano a bangarori da dama

Kwamishinan lafiya ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su cigaba da kula da matakan kariya daga yaduwar cutar sarkewar numfashi ta wanke hannu akai-akai da kuma sanya safar fuska.

Exit mobile version