Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Tsarin Ba Ma’aikata Bashi

Daga Mustapha Ibrahim Kano

Yanzu haka ma`aikatan Jihar Kano sama da 2,600 ne su ka samu bashin kuɗi daga Naira dubu 30 zuwa dubu 90 da kuma dubu 50, domin su je su sayi abin hawa dai-dai da ƙarfin ma`aikaci da kuma buƙatarsa.

Wannan bayani ya fito daga bakin Farfesa Kabiru Isa Ɗandago kwamishinan kuɗi mai barin gado, a lokacin da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci ƙaddamar da ba da bashin ga ma`aikatan Kano da kuma raba ma mata da matasa sama 500 kayan sana`oi da a ka tallafa musu da su, bayan an horar da su sana`o`i na watanni, a bikin da aka gudanar a cikin gidan gwamnatin.

Haka kuma Farfesa Ɗandago ya ce, ba wannan ne karo na farko da Gwamna Ganduje ya fara ba ma`aikatan bashi ba, sai dai wannan karon an yi biki ne saboda yawan ma`aikatan da aka ba bashi a wannan lokaci, an kuma yi hakan ne saboda sauran jihohi da hukumomi su yi koyi da wannan aikin alhairi na gwamnatin Kano.

A na shi jawabin, Kwamishinan yaɗa labarai da al`adu da wasanni, Malam Muhammad Garba ya ce, ƙoƙarin Gwamnan Kano ya fito fili a ƙasar nan, kuma wannan ya kawo adadin mata sama dubu 20 da aka koyawa sana`a daban-daban kuma aka basu kayan sana`a kyauta domin samar da aiki a tsakanin su da kuma yaƙar talauci kamar yadda gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin

Exit mobile version