Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Ba Matasa 8,800 Tallafin Miliyan 275

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shelanta cewa, gwamnatin Jihar ta kashe jimillan Naira milyan 275 kan abubuwan da suka shafi karfafa matasa.
Gwamna Ganduje, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, sa’ilin da yake kaddamar da sabon shirin bayar da tallafin kudade ga matasa 8,800, a gidan gwamnati da ke Kano.
A cewar sa, ana bayar da tallafin ne domin karfafa matasan su kafa sana’o’in su domin su kasance masu dogaro da kawukan su.
Gwamnan ya ce, “Jimillan matasa 8,800 ne da suka fito daga dukkanin kananan hukumomi 44 na Jihar za su amfana da shirin, inda kowane matashi guda zai karbi Naira dubu 20,000.
“Sannan wasu sashen 6,600, kuma da suka kumshi mata zalla za su amfana da shirin, inda kowacce daga cikin su za ta karbi Naira dubu 15,000,” in ji Ganduje.
Gwamnan Jihar ya ce, wannan shirin bayar da tallafin da gwamnatin Jihar ta fito da shi, tabbas ya rage zaman banza, aikata laifuka da makamantan su a Jihar.
Kan haka, sai ya bukaci matasan da su tabbatar sun zabi Shugaba Buhari a babban zabe mai zuwa na 2019.
Tun da farko a na shi jawabin, Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na Jihar, Alhaji Murtala Sule-Garo, cewa ya yi, an fito da shirin ne domin ya magance matsalar zaman banza ga matasan Jihar.
Kwamishinan ya ce, shirin zai tallafi na gwamnatin tarayya wajen magance rashin aikin yi musamman ga matasan kasar nan.
Ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: