Daga Abdullahi Muhammad,
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya bayyana bukatar da ake da ita ga Alhazan Jihar Kano da su zama jakadu na gari alokacin gudanar da aikin Hajji. usaman Allah Alhaji na wannan bayanibne alokacin kaddamar da bitar alhazai na wannan shekara, Wanda aka gudana a makarantar koyar da harshen larabci, wato SAS a birnin Kano.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Wanda shi ne ya wakilci Gwamnan Jihar Kano, Dakat Abdullahi Umar Ganduje, OFR, (Khadimul Islam). Ya kara da cewa jama’ar Jihar Kano mutane be Masa lura da doka da oda, sannan kuma ga yakana, wannan tasa duk shekara Jihar Kano ta zakarar gwajin dafi, wacce ake kwaikwayo aduk wasu tsare tsaren aikin Hajji.
Haka Alhaji Usman Alhaji ya ja hankalin maniyyatan da su bada hadin kai da goyon baya, musamman batun Rigakafin annobar Korona, yace jama’ar Kano shaidane sun ga Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje tuni ya karbi tasa allurar agaban jama’a.
Shi ma Mai martaba Sarkin Kano Kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Allah Ya kara was sarki lafiya, ya bukaci mahajjata da zasu tafi saga Jihar Kano da cewa su Zama wakilai nagari musamman wajen kiyaye dokokin Hukumar Alhazan kasar Saudiyya domin samun gudanar da ingantancen aikin Hajji.
Daga cikin manyan mutane wadanda Allah ya nufe su da halartar wannan taro mai mahimmanci da dimbin tarihi. Akwai kwamishiniyar Mata da walwala, Dr Zahrau Umar Muhammad, tsohon Manajan Daraktan tashoshin jiragen ruwan Nujeriya, Alhaji Aminu Dabo, Shugaban karamar hukumar birni, Alhaji Fa’izu Alfindiki tare da sauran shuwagabannin kananan hukumomin Jihar Kano.