Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Bisa la’akari da daminar da ake ciki mai girma Gwamna Ganduje ya tabbatar da farfado da kamfanin gidan gona na KASCO wanda ya yi fice ta fuskar samar da takin zamani mai inganci. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar gona na Jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a wata ganawa ta musamman da wakilinmu a Kano.
Ya ce a matakin farko, mai girma Gwamna Ganduje ya turaw a wannan kamfani kudi Naira milyan dari biyar domin sayan sinadarin aikin samar da takin zamani, yanzu haka wannan kamfani ya ci gaba da aiki inda ake sayar da takin kan farashi mai rahusa daga kan naira 5,500.
Haka nan, ya ce gwamnati ta bayar da tirela 484 na takin zamani ga kananan hukumomin jihar Kano 44, tare da cewa a wannan shekarar Gwamnan jihar ya bayar da umarnin yin sassauta farashin takin daga naira 5,500 zuwa 5,000. Sai kuma tsarin da gwamnatin Kano ta yi don amfani manoman rani inda ta ba su rance mai saukin ruwa.
Ta bakin kwamishinan, “Ina tabbatar da cewa kasuwanni a wannan shekara za su tumbatsa da kayan abinci, wanda har sai mun sayar wa makwabtanmu a kasashen waje”.
A karshe, Dakta Nasiru Gawuna ya jaddada aniyar Gwamna Ganduje na ganin matasa kowa ya amfana da kyawawan tsare-tsaren wannan gwamnati.