Mashawarciya ta musamman kan Harkokin lafiya Dr. Fauziyya Buba Idris ce ta bayyana haka a ranar Lahadin data gabata alokacin tattakin Kungiyoyin da ofishinta ya shirya mai taken “Kawar da babbancin Jinsi da yaki da matsalar tauye Hakkin Yara.”
Tattakin da aka gudanar daga fadar Sarkin Kano aka wuce ta ofishin shugabar ma’aikatan Jihar Kano daganan aka wuce zuwa gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Dr. Fauziyya Buba tace wannan tattakin baiwa muhimmanci kadai ba, har ma da kasancewar an gudanar dashi alokacin da ake fatan samar tubali da zai taimaka wajen dorewar cigaban Jihar Kano.
Ta kara da cewa, taron nada alaka da kaucewa kowane irin salon cin zarafin Mata da Kananan Yara a Jihar Kano da ma Kasa bakidaya.
Gwamnan Jihar Kano wanda Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata Dr. Zahra’u Muhammad ta wakilta tace, mai girma Gwamna na tabbatar da ganin ya bada goyon baya ga masu ruwa da tsaki kan duk wani al’amari da zai taimaka wajen warware abubuwan dake damun al’umma abaya da kuma yanzu.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Wanda Dan Kadan Kano, Dr. Bashir Muhammad ya wakilta ya ce, dukkanin masarautun Kano biyar na kin jinin Batun wariyar jinsi da Kuma keta hakkukukuwan kananan yara.
Tattakin da aka gudanar acikin makon da ya gabata, ya samu halartar kungiyoyin kwararru, wadanda suka hada da likitoci, Lauyoyi, Mata ‘yan Jaridu, kungiyoyin sa Kai, CSO’a, FBO’s, Mwan, FIDA, NAWOJ, masu bukata ta musamman, HILWA wadanda suka fito daga sassan daban daban na harkokin rayuwar al’umma. Kamar yadda jami’in yada labaran ofishin mashawarciyar na musamman Auwalu Musa Yola ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.