Daga Abdullahi Muhammad, Sheka
A cikin makon da ya gabata hukumomi a Jihar Kano suka kara jaddada dokar hana goyo a babur a fadin Jihar Kano, dokar da aka kafa tun a shekara ta 2013 lokacin Marigayi Sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero, bayan wani farmaki da aka kai wa tawagar sarkin a lokacin da ya halarci saukar karatun Alkur’ani a masallacin Murtala da ke Jihar Kano.
Yanzu haka dai a iya cewa, kwanciyar hankali ya dawo a Jihar Kano, wanda hakan yasa masu ababen hawa ke amfani a wasu lokuta suna rage wa ‘yan uwa, iyalai da ma abokan arziki hanya a lokutan tafiye-tafiyensu. Amma kwatsam bayan jama’a hankali ya kwanta sai aka wayi gari da wata sanarwa da ke nuni da cewa an sabunta dokar da ta hana goyo akan babur a fadin Jihar Kano.
Sanarwa ta nuna duk wanda aka kama da goyo akwai tarar naira dubu goma, wannan sanarwa ta fama wa al’ummar Jihar Kano ciwon da tuni suka sa ran warkewarsa, domin wannan sanarwa sai ta nuna kamar ana shirin komawa gidan jiya ne.
Yayin taron, manema labarai sun gane wa idanunsu daruruwan baburan da hukumar ta damke, kuma kamar yadda aka tsegunta wa manema labarai duk wanda aka kama ana tilasta masa biyan tarar naira dubu goma matukar yana bukatar abin hawanasa ya dawo hannunsa.