Shugabancin kamfanin sarrafa shinkafa mai suna Tiamin Rice Limited a ranar Lahadi ya bayyana cewa, gwamnatin Kano ta umarce shi da ya kulle masana’antar tasa kan zargin gurbatacciyar iskar da kamfanin ke fitarwa, inda ta ce iskar ce ke ta’azzara rashin lafiyar masu fama da cutar Korona a jihar.
Ana iya tuna cewa, a jawabin da ya yi wa ’yan Nijeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire duk wasu kamfanoni da su ke sarrafa abinci daga dokar cigaba da gudanar da ayyukansu, domin a rage radadin cutar a kan ’yan kasa da kuma tabbatar da yalwar abincin.
A martaninsa kan umarnin rufewar, Mataimakin Babban Manajan kamfanin,
Aliyu Ibrahim, ya ce, zargin na gwamnatin ba shi da tushe, musamman ma duba da cewa nisan sama da kilomita 20 ne tsakanin kamfanin da cibiyar killace masu cutar Korona din da ke filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mataimakin Babban Manajan ya nuna cewa, akwai masana’antun sarrafa shinkafa kusan 30 da su ke aiki a jihar, inda ya yi mamakin dalilin da ya sanya kamfaninsa ne kawai ya tsone wa gwamnatin ido.
Ya bayyana cewa, shugabancin kamfanin ya samu takardar da gwamnatin ta aiko ne ta hannun Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Jiha a ranar 18 ga Afrilu, 2020.
Ya ce, ”mun samu sakon matakin da gwamnati ta dauka ta mu rufe kamfaninmu ne a wata ‘Sanarwa ta Rufewa’ ran 18 ga Afrilu, 2020, inda ta kawo ma na.”