Abdullahi Muhammad Sheka">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Kano Ta Musanta Rushe Gadar Kofar Nasarawa

by Abdullahi Muhammad Sheka
February 17, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Gwamnatin Kano Ta Musanta Rushe Gadar Kofar Nasarawa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnatin Kano ta ce ko kacan bata da shirin rushe gadar kofar Nasarawa illa iyaka wasu ‘yan gware-gyare da za yi a jikin gadar.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ta cikin shirin ‘Barka da hantsi’ na gidan rediyo freedom ranar Litinin.
Muhammad Garba ya ce ko kadan ba a ce za a rushe gadarba, illa iyaka gyare-gayare da aka ce za a yi a jikin gadar da ake ganin tana bada barazana.
Ya ce, ya yi bayani ne a baya kan halin da gadar ke ciki, inda ya ce masana na nan na hada bayani kan halin da gadar ke ciki, na matsalolin da ake ganin ta samu.
Garba ya ce da zarar sun karbi sakamakon binciken, za su yi amfani da bayanin wajen gyara duk abinda suka bijori da shi.
Idan za a iya tunawa dai, tun a ranar Taladar da ta gabata ne Muhammad Garba ya ce akwai yiwurar rushe gadar sama ta kofar Nassrawa sakamakon zaizayewar da ta fara yi.
Muhammad Garaba ya sanar da hakan ne lokacin da yake karbar kungiyar ‘Ganduje raya Kano yake’.
Ya ce, tuni suka shiga nazari tare da kwararru kan irin matsalolin da gadar ke haifar wa ga al’ummar Kano.
Ya kara da cewa gadar ta fara zaizayewa saboda rashin kyawun aikin da aka yi, tana kuma hada cunkoso.
Kwamishinan ya ce, da zarar kwararru sun gama nazari a kai, Gwamnati za ta duba yiwuwar rushe gadar tare da sake ta. Sai dai kwamishinan ya ce jama’a basu fahinci abinda kalaman nasa ke nufi ba.
Ya ce za su yi aiki ne da bayanan kwararru, da kuma shawarar da suka bayar, idan ma takama a rushe wani bangare na gadar domin a yi gyara to za a rushe, amma ba rusheta baki daya ba.
Muhammad Garaba ya ce ‘yan Kwankwasiyya basu da wani abu da za su nuna ko tunkaho da shi da ya wuce gadar.
“Saboda firgita da ‘yan hamayya suka yi, yan PDP yan Kwankwasiyya, saboda babu wani abu da suke da shi da za a iya gani a taba a fadin jihar Kano illa iyaka wanna gadar. “Wannan gada inda kasan rayukansu haka take, saboda haka suka kidime baki dayansu, sukai ta shiga gidajen rediyo sunata kalubalantar abin.
“Mu abinda muke cewa ,ai kaga bayani ne na hankali, bayani ne mai gamsuwa, duk wanda yasan me ya ke yi zakaga cewa koma wace Gwamnati ce, ko dama Gwamnatin su ce ke mulki, indai Gwamnati suke ta hakika aka ce wannan abu zai iya kawo hadari, kuma abu na karshe da ya kamata a yi shi ne a yi kaza, na tabbatar indai Gwamnati na jama’a ne za su duba su gani.
“Na riga naji duk kalubalen da ake yadawa na Biliyon shida da aka gina wannan gada, idan aka rusheta ina za a samu a sake ginata. Amma kamar yadda na fada ai ba cewa nayi Gwamnati ta zauna ta yi nazarin rahoton, wannan shi ne abuna.
“idan har ta kama cewar za a iya gyara wasu daga cikin wuraren da ya tsuke, duk irin wadannan gyare-gyaren idan ta kama za a gyara ba tare da anzo matakin da za a ce an ruguza ba. Amma wallahi ni ban yi magana ta siyasa.”

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnan Neja Ya Taya Gwamnan Kaduna Murnar Cika Shekaru 61 Da Haihuwa

Next Post

Noman Alkama: Gawuna Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Masu Ruwa Da Tsaki

RelatedPosts

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

by Abdullahi Muhammad Sheka
2 days ago
0

Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

by Abdullahi Muhammad Sheka
2 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri Biyo bayan harin da mayakan Boko...

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

by Abdullahi Muhammad Sheka
2 days ago
0

Daga Musa Muhammad, Abuja An kammala dukkan shirye-shirye don fara...

Next Post

Noman Alkama: Gawuna Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Masu Ruwa Da Tsaki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version