Sulaiman Ibrahim" />

Gwamnatin Kano Ta Rufe Masallacin Sheik Abduljabbar Kabara, Ta Hana Shi Wa’azi

Gwamnatin Kano ta umarci Shiekh AbdulJabbar Nasiru Kabara da ya dakatar daga gabatar da duk wani nau’in wa’azi a fadin jihar, tare da umarnin rufe masallacinsa mai suna As-habul kahafi dake unguwar Sani Mai Nagge
Kwamishinan watsa labaran jihar ta Kano Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a daren jiya Laraba, inda yace matakin ya soma aiki ne anan take.

yayin ganawa da manema labarai, kwamishinan yace umarnin kan Shiekh Abduljabbar ya zama dole, sakamakon rahotannin kalaman tunzura jama’a da rashin kan gado da fitaccen malamin ke yi, yayin gabatar da wa’azinsa.

Exit mobile version