Daga Ibrahim Muhammad,
A kokarin da Gwamnatin jihar Kano ke yi wajen bunkasa harkar koyar da inganta lafiya, Kwamishinan ma’aikatar lafiya, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya jagoranci bude sabon asibiti a Kwalejin kimiyyar lafiya da tsaftar muhalli ta jihar, wanda zai taimaka a fannin kula da lafiyar dalibai da samun horo da kwarewa a harkar karatunsu.
A yayin taron bude asibitin, Kwamishinan ya yaba wa Hukumar gudanarwar Kwalejin, karkashin jagorancin Dokta Bishir Bala Getso bisa samar da managartan dalibai da ke tallafa wa bunkasa harkar lafiya, ba a jihar Kano kawai ba, harm a a sassan fadin kasar nan.
Ya ce, saboda damuwa da Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke yi wajen inganta harkar lafiya ya sa ta gina wannan asibiti a harabar Kwalejin domin ya taimaka wajen samar da tantancewa na wasu kwasa-kwasai da aka fito da su sababbi da za su taimaka wa wannan makarantar, kuma asibitin zai bada dama ga marasa lafiya a bangaren dalibai da ma’aikata na makarantar da ma sauran al’ummar da ke makwabtaka, su amfani asibitin.
Shi ma da yake nasa jawabin a lokacin bude asibitin, Shugaban Kwalejin, Dokta Bashir Bala Getso ya yaba wa Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarinta wajen inganta harkokin koyo da koyarwa aikin lafiya a fadin jahar.
Ya kara da cewa, Kwalejin ta tura neman karin kwasa-kwasai guda shida, kuma Gwamnatin jihar ta sahalle musu guda Uku ganin cewa sai an sami karin fadada makaranta sun mika wa Gwamnati bukatar, kuma tuni sun taba alli da Gwamnati wajen.ganin cewa sun.sami karin wani bangare na fadada kwalejin a wajen kwaryar Kano, wanda suna sa ran bada dadewa ba, zai tabbata domin har sun je ma sun yi kewaya a wajen suna jira ne a sami tabbatarwar Gwamnati.
Daga nan Dakta Bashir Bala Getso ya yaba wa Kwamishinan lafiya na jihar, bisa irin goyon bayan da yake baiwa ci gaban kwalejin, tare da kira ga dalibai su dage wajen yin amfani da cibiyar kula da lafiyar don samun kwarewa a harkar lafiya.