Gwamnatin Kano Ta Samar Da Famfunan Ban Ruwa 3,000 Don Inganta Noman Tumatir

Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana aniyar Gwamnatin Dakta Abdullahi UmarGanduje na samar da Injunan Ban ruwa 3,000 domin inganta noman tumatir tare da sauran kayan amfanin Noma domin tabbatar da sabunta tsarin Noma a Jihar Kano.
Dakta Gawuna ya kara da cewa yanzu haka Gwamnatin Jihar Kano ta samar bashin Dala Miliyan dubu 95 daga Bankin cigaban harkokin Noma wanda daga cikin wannan adadi kaso 50% zai tafi bangaren harkokin noman Rani.
Dakta Nairu Yusif Gawuna na wannan Jawabi ne ga manema Labarai a lokacin da yake zagawa da Minstan Hakokin Noma na Nijeriya Audu Ogbe da Gwamnna Babban Bankin Kasa Mr. Godwin Emepele a lokacin ziyarar dasu ka kai kamfanin sarrafa Tumatir na Dangote dake Kadawa cikin Karamar Garun Malam.
Ya ce, Gwamnati zata ci gaba da hada hannu da Kamfnin na Dangote ya c,e muna yin duk abinda ya kamata domin samar da kyakkyawan yanayin gudanar da hakokin noman rani a Jihar Kano.
Ya ce a anan Kadawa mun samarwa da Kamfanin na Dangote sama kadada 200 yayin da a garin Danbatta wannan Gwamnatin ta samar da wasu karin kadada 400 domin inganta noman tumatir . Gawuna ya ci gaba da cewa wannan kokari na Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganuje ya zo a lokacin da ake kaddamarn da sabbin tsare tsaren kara samar da abinci, karin
kudaden shiga ga kananan Manoma, ingancin tsaro tare da shirin nan na kawar da talauci a tsakanin matasa.
Mataimakin Gwamnan Dakta Nasiru Yusif Gawuna wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar harkokin Noma na Jihar Kano ya ci gaba da bayyana cewa daukar nauyin ire iren wadancan shirye shirye zai taimakawa shirin gwamnati na tallafawa matasa tunda matakin farko.
Gawuna ya ce Gwamantin Dakta Abdullahi Umar Ganduje zata ci gaba da ta tallafawa harkokin gwamnatin Tarayya karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari musamman kan shirinsa na farfado da harkokin Noma domin amfanin kananan Manoma.
Da Yake Jawabi a lokacin taron Ministan harkokin Noma na Tarayyar Nijeriya Audu Ogbe cewa ya yi wannan Gwamnatin zata ci gaba da mayar da hankali wajen bayar da dukkan tallafi ga Bankin Manoma domin baiwa manoma damar samun rancen kudi mai ragwame. Ya ce muna fatan shiga sahun wadan da ke sahun gaba wajen samar Tumatir a fadin Duniya domin rage dogaro da wasu hanyoyin samar da Tumatir a Nijeriya.
Ya ce dole a karfafi Kamfanin Alhaji Sani Dangote da kuma sauran nagartatun manoma a Jihar Kano domin tabbatar masu da aniyar Gwamnatin tarayya kan duk wasu alkawuran sake fasalin harkokin noma sun tabbata.
Shima Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Mista Godwin Emepele taya murna ya yi ga hukumar gudanarwa Kamfanin Gonar ta Dangote bisa jajircewa kan harkokin samar da tumatir, wanda wannan shi ne kamfani daya tilo a Nijeriya.
Ya ce za su tabbatar da cigaban aikin wannan kamfani a kullum.Ba karamar nasara bace da ya kamata ayi alfahari da ita, wannana tasa bayan doguwar tattaunawa da a ka yi das hi mu kayi kokarin fahimtar da sauran Bankuna domin bashi dukkan gudunmawa, wanda yanzu haka guda daga cikin wadancan Bankuna ya amince da shigo da Green House domin cigaban ayyukan kamfanin, inji Emepele.
Tunda farko wakilin Gonar ta Dagote Alhaji Sani Dangote ya tabbatar da cewa da gudummawar Babban Bankin Kasa (CBN), Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Ma’aikatar harkokin ciniki da masana’antu ta tarayya da kuma Gwamnatin Jihar Kano cewar hana shigo da tumatir daga Kasashen waje zai bai wa manaoman tumatir damar mayar da hankali tare da amfanar noman tumatir din acikin kasa Nijeriya. Kamar Yadda mai Magana da yawun ofishin Mataimakin Gwamnan Kano Hassan Musa Fagge ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau.

Exit mobile version