Daga Mustapha Ibrahim , Kano
An bayyyana cewa ba a yadda waniKwamishina ko jami’in ilimi yayi amfani da kudin da aka bayar na tallafin ilimi ga‘yan mata ba.Wannan bayani ya fito ne daga bakin kwamishinan ilimi kimiya da fasaha kuma mataimakin gwamnanKano, farfesa Hafizu Abubakar a lokacin wani taro na kaddamar da bayar da tallafi ga yara mata marasa galihu domin su cigaba da Iliminsu, Taron wanda ya gudana a dakin taro na ‘Coranation’ dake gidan gwamnatin kano.
Tallafin dai ya fitone daga kungiyoyin tallafin Ilimi na Majalisar Dinkin Duniya, domin a tallafawa yara masu rauni wurin samun ingantaccen ilimi, kuma adadin kudin da aka bai wa Nijeriya ya kai Naira miliyan 100.
Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewa wannan dudi an ba da su ne domin tallafawa yara mata don su samu Ilimi kamar yadda ya kamata, don haka ba a yadda ba, kuma ba a yafewa duk wani Kwamishina ko wani jami’in ilimi da yayi amfani dawannan kudi domin kansa ko da na shan lemon kwalba ne.
Haka kuma ya ce irin wadannan yara da zasu ci gajiyar wannan lamari zai yi tasiri sosai a rayuwarsu kuma za ayi amfani da wannan tallafine bisa sharadin da wadannan kungiyoyi suka bayar na bayar da litattafai da gyaran azuzuwa,domin kula dasu yadda yakamata dadai sauran abubuwa da zasu inganta ilimin mata marasa galihu.