Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Sayar Wa Kamfanin ‘Mudatex’ Otel Din Daula

Published

on

Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta mika dadadden katafaren ginin nan na otel din Daula da aka mai da ita makaranta ga kamfanin Mudassir & Brother domin ya zama wajen kasuwanci.
Shugaban Kanfanin na Mudassir & Brother Alhaji Mudassir Idris da aka jiyoshi yana mika godiya ga Gwamnan jihar Kano a yayin bude sabon ginin kamfanin na hada hadar kasuwancinsa akan titin Ibo dake daura da kasuwar Sabon gari a jiya Asabar.
Kamfanin na Mudassir & Brothers ya ce, nan gaba kadan zasu sake kiran wani taron makamancin wannan domin bude wani katafaren reshen a otel din na Daula daya zama mallakinsu a yanzu.
Shi dai otel din na Daula an gina shi ne a zamanin mulkin Gwamnan Kano Audu Bako a cikin shekara ta 1973.
A zamanin Gwamnatin mulkin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso karo na Biyu ne ya maida otel din sashin tsangayar karatun yawon bude ido a karkashin jami’ar Kimiyya da fasaha ta Wudil.
Jama’a da dama a jihar Kano sun nuna rashin gamauwarsu da wannan mataki da Gwamnatin ta yi suna ganin cewa hakan koma baya zai jawo ga harkar ilimi.
Sai dai wasu na ganin hakan zai dada taimakawa cigaban kasuwanci.
Advertisement

labarai