Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Gwamnatin Kano Za Ta Gina Wa Soji Filin Atisaye A Dajin Falgore

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ranar Juma’a ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata gina filin atisayen sojoji wanda ya kai na Naira miliyan 318 a dajin Falgore inda yanzu ya zama wajen fakewar yan ta’adda. Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin rufe bikin gasar sojojin bataliya ta daya da aka gudanar a barikin soji na Bakuvu dake Kano.

Gwamnan ya ce, ‘idan sojoji na dajin to ‘yan ta’adda da masu gakuwa da mutane da sauran kungiyoyin yan ta’adda zasu ji tsoro su bar dajin. Zamu dora tushen ginin wannan muhimmin aiki kwanannan kuma zai zama gagarumar nasara wajen magance matsalolin tsaro a yankin.’

Ya kara da cewa gwamnatinsa zata fito da tsari mai kyau don ganin an tabbatar da an samar wa da alumma tsaro garuruwan tsaro.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar zata zauna da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Tudun Wada a inda dajin na Falgoe yake. Gwamnan ya kara da cewa gasar da sojojin suka gudanar ya kara tabbatar da kokarin sojin na ganin cewa sun magance matsalolin tsaro a kasar nan.

Har ila yau, babban sojin bataliyar, Maj-Gen Faruk Yusuf ya ce gasar na da zummar karawa sojoji sanin dabarun yaki, hadin kai, da kuma shugabanci da dai sauransu. Hukumar Sojin Nijeriya za ta cigaba da maida hankali kan atisaye don ganin cewa dakarunta sun sauke nauyin da aka dora masu.

Yusuf yayi amfani da wannan daman wajen godewa gwamnatin jihar bisa da ta gina masu gidaje guda 30 a Barikin Bukavu da kuma ta

Exit mobile version