Gwamnatin Kano Za Ta Kula Da Masu Fama Da Ciwon Ido Kyauta

Daga Ibrahim Muhammad Kano,

Masu larurar idanu 14,000 ne za su amfana da aikin duba idanu da bada magani da samar da gilashi kyauta a Jihar Kano.

Kwamishinan ma’aikatar lafiya na Jihar Kano, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana haka a yayin hira da manema labarai da aka gudanar a kan zagayowar ranar gani ta duniya a dakin taro na ma’aikatar lafiya.

Ya ce, ranar idanu ana yi ne dukkan Alhamis ta biyu ta watan Oktobar duk shekara kuma duba masu larurar zai gudana ne a dukkan masarautu biyar na jihar.

Ya ce, taken burin shirin na wannan shekarar shi ne “Muso Idanuwammu” alkaluma sun nuna cewa kashi 90 na larurar idanu ana samu ne a kasashen Afirka, mafi yawanci kuma yafi shafar mata. Larura ce kuma da za a iya kare kai daga kamuwa wadanda suka kamu kuma za a iya magance ta.

Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce Jihar Kano ta fara shig bikin wannan ran ace tun shekarar 2019 an kuma yi wa masu larurar 16,000 magani kyauta. Wannan karo na za a yi gangami na duba idanu a yi musu aiki da basu gilasai da magunguna.

Ya ce, yanzu haka Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta sanya kayan aikin kula da lafiyar idanu a asibitoci da baiwa ma’aikata horo don rage larurar idanu.

Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa yace Gwamnatin jahar Kano ta bijiro da baiwa da dama domin kulada lafiyar al’umma a matakai daban-daban ciki akwai samarda lafiya kyauta da Mata masu juna Biyu da kananan yara da kuma wadanda suka gamu da hatsari.

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya kaddamar da soma kula da masu larurar idanun kyauta a Asibitin Murtala da ke cikin birni.

Exit mobile version