Sagir Abubakar" />

Gwamnatin Katsina Na Shirin Kafa Kotun Hukunta Alhazai

Daga Sagir Abubakar, Katsina

Gwamnatin jihar Katsina za ta duba yiwuwar kafa kotu ta musamman domin  hukunta maniyyata Hajji da ke aikata laifuka daban-daban lokacin gudanar da aikin Hajji.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka bayan ya amshi rahoton Kwamitin aikin Hajjin shekarar da ta gabata daga hannun shugaban Kwamitin kuma Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Mannir Yakubu.

Gwamnan ya bayyana cewa kafa wannan kotu zai ba da damar hukunta duk wanda  aka samu da aikata ba dai-dai ba walau Ma’aikaci ko Mahajjaci.

Tun farko a nashi jawabin, Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana aikin Hajjin na shekarar 2017 a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi samun nasara duk kuwa da matsalolin da aka samu wanda kuma dukkan su sun afku ne saboda jinkiri wajen shirye-shiryen aikin.

Ya kuma kara da cewa Kwamitin ya ba da duk shawarwarin da suka kamata domin kiyaye sake fuskantar matsaloli a ayyuka na shekaru ma su zuwa.

Tun da farko sai da shugaban tagawar aikin hajjin, Mai shari’a Musa Danladi Abubakar ya bayyana cewa duk da irin da nasarorin da aka samu a ya yin aikin Hajjin an samu wasu matsaloli da ya kamata a dubu ba sosai domin dauka matakin da ya kamata.

Ya kara da cewa an samu wasu maniyata sun nuna halayyar rashin da’a a lokacin wannan aikin Hajji inda suka tunzura wasu suka yi wata zanga-zanga wanda ta nuna rashin da’a da  kin bin umarnin shuwagabannin aikin hajjin.

Mai shari’a Musa Danladi Abubakar ya kara da cewa tawagar maniyatan na bara sun ba da shawarar cewa ya kamata gwamnatin  jihar Katsina ta kafa wata kotu ta musamman domin hukunta wadanda suka aikata wani laifi a yayin aikin Hajji da suka hada da maniyata ko kuma shuwagabannin tafiyar.

A cewarsa, wannan kotun akwai irin ta a wasu jihohi da suka hada da Kano kuma ya bayyana cewa ana aiki da wanna kotu domin kara kyautatta tafiyar da aikin hajji a sauran jihohin Nijeriya.

 

 

 

Exit mobile version