Gwamnatin Katsina Ta Kafa Jami’an Tattara Bayanai Kan Harkokin Ilimi

Harkokin ilimi

Daga Sagir Abubakar,

Yanzu haka jami’an tattara bayanan harkokin ilmi na jihar Katsina na samun horon sanin dabarun aiki.

Hukumar ilmin bai daya ta kasa hadin gwiwa da ta jihar Katsina suka shirya taron.

Da yake buda taron shugaban hukumar ilmin bai daya daya samu wakiltar sakataren hukumar Alh. Isah Mohd Musa ya bayyana godia ga hukumar UBEC akan shirya taron.

Alhaji Lawal Buhari ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta samar da na’u’ra mai kwakwalwa ga jami’an tare da horas dasu akan amfani da manhajar kobo collect don tattara bayanai.

Alhaji Lawal Buhari Daura shugaban hukumar ilmin bai daya ta jiha yace an bude adireshin yanar gizo a hukumomin ilmin na kananan hukumomi talatin da hudu na jiha Alhaji Lawal Buhari Daura.

Ya kuma bukaci mahalarta taron dasu maida hankali ta yadda zasu samu karin ilmi akan aikin su.

Da take jawabi jami’ar hukumar ilmin baidaya ta kasa a jihar Katsina Hajia Maryam Audi Kankara tace ana amfani da sahihan bayanai wajen inganta ilmi.

Shima da yake jawabi, jami’in kula da ingancin ilmi Umar Dauda yace taron horaswar nada nufin tabbatar da cewa bayanan da ake tattarawa na da sahihanci.

Ya kara da cewa taron zai baiwa mahukunta damar tattara bayanai da kuma dokar matakan da suka dace don bunkasa ilmi a kasa.

Exit mobile version