Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Katsina Ta Kammala Gina Sabuwar Kasuwa Da Tashar Mota A Funtuwa

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta kammala gina sabuwar kasuwa da tashar mota ta zamani a Funtuwa dake jihar Katsina, aikin gina kasuwar hade da tashar wadda Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ta gina mai kimanin shaguna dari tara.

A lokacin da mai baiwa Gwamna shawara akan harkar kasuwanci Alhaji Abubakar Yusuf yake duba yadda aka gudanar da aikin ya yaba ma mai girma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari akan irin hangen nesa da ya yi wajen gina wannan babbar kasuwa hade da tashar mota ta zamani abin a yaba ne kuma babu shakka kasuwancin yankin zai kara habaka kuma ya yaba ma yan kwangilar irin yadda suka gudanar da aikin cikin lokaci kuma ingantacce.

Mai baiwa Gwamna shawara akan harkar kasuwanci yaci gaba da cewa babu shakka Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ta yi kokari wajen gudanar da manyan aiyuka a fadin jihar kuma babu wani bangare da Gwamnatin Alhaji Aminu Bello bata tabo ba musamman wajen kiwon lafiya, aikin gona, harkar kasuwanci, hanyoyin daukar matasa aiki da sauran manyan ayyuka a dukkan fadin jihar.

Alhaji Abubakar Yusuf ya ce, Gwamnatin Alhaji Aminu Bello za ta bi dukkan hanyoyi na gaskiya don tabbatar da adalci wajen raba shaguna musamman wadanda aka rushe shagunansu don su sake mallakarsu, Ya yabawa al’ummar jihar wajen bada goyon bayansu ga wannan Gwamnati, ya kuma ce su cigaba da goya mata baya kuma mutane su guji yada jita jita marasa amfani ga al’ummar su guji saka siyasa a harkar Gwamnati ko bata Gwamnatin don bambancin siyasa.

Alhaji Abubakar Yusuf ya kuma ce, Gwamnatin za ta sa ido sosai wajen tsaftace kasuwar da tashar mota, Gwamnati ba za ta yarda da kafa rumfuna acikin kasuwar ba dole abi doka da oda wajen tafiyar da kasuwar.

Alhaji Abubakar Yusuf ya kewaya kasuwar tare da sauran jami’ai daga ma’aikatar kula da harkar kasuwanci da jami’an karamar hukumar Funtuwa da Sarkin Maska hakimin Funtuwa Alhaji Sambo Idris Sambo da shuwagabannin yan kasuwa na shiyyar Funtua Alhaji Ibrahim dan Suleiman Sheme da shuwagabannin ‘yan kasuwar Funtua a karkashin shugabancin Alhaji Musa shugaba da Alhaji Kabir Rawayau da shuwagabannin kungiyar direbobi ta kasa shiyyar Funtuwa karkashin jagorancin Alhaji Hamisu Miloniya da Alhaji Musa K S shugaban kungiyar direbobi ta Funtuwa NURTW da Alhaji Babangida Agasache da sauran Jami’an tsaro na karamar hukumar.

Daga karshe Alhaji Ibrahim dan Suleiman Sheme ya mika godiyarsa ga Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari yadda ya gina masu babbar kasuwa hade da tashar mota ta zamani a Funtuwa don habaka kasuwanci a yankin da sauran manyan ayyuka a fadin jihar.

 
Advertisement

labarai