Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta shirya tsaf domin maida duk wani nau’in biyan kudadan haraji ta hanyar zamani domin yin gogayya da sauran jihohi a wannan sabuwar fasaha ta zamani da aka dade da fara amfani da ita.(Computarisation system)
Shugaban hukumar tatara kudadan haraji na jihar Katsina, Alhaji Abdulmumini Dan Rabati Aminu ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsina tare da fadin cewa yanzu shiri ya yi nisa wajan aiwatar da wannan kudiri na su.
Haka kuma bayyana cewa duk abinda ake bukaka domin yin wannan aiki gwamnatin jihar Katsina ta saya ta sanya shi a sabuwar shelkwatar hukumar da ta gina wanda take shirye-shiryen tarewa ba da jimawa ba.
Ya kara da cewa kayayakin zamani wadanda za a yi aikin tattara kudadan haraji tuni an sayo kuma an zuba a wasu ofisoshin hukumar da ke sauran ma’aikatun gwamnatin a fadin jihar Katsina.
Kamar yadda ya bayyana ya ce a bangaran kudadan harajin da suke karba a wurin manoma dole tasa suka rage shi da kashi 50 wasu kuma da kashi 20 sakamakon yanayin da aka shiga na cutar korona da ta sanya duniya
“Idan muka duba wannan batu na korona ba wai ya shafi maganar tattara kudadan haraji ba, a’a ya shafi duk wani al’amari na tattali arzikin jihar Katsina da Najeriya da ma duniya baki daya.” Inji shi
Alhaji Abdulmumi Dan Rabati ya ce baya ga tattara kudadan haraji da hukumar take yi ta kuma yi wasu ayyukan na musamman kamar gina sabuwar shelkwatar hukumar da gyara wasu ofisoshinta da ke shiyoyi uku na jihar Katsina.
“Haka kuma mun gina sabuwar shelkwatar wannan hukuma akan kudi naira miliyan 607 wanda yanzu haka aikin ya kai matakin kashi 81 kuma an biyan dan kwangila naira miliyan 439 domin samun ikon gudanar da aikinsa cikin nasara” inji Dan Rabati
Yace sun baiwa kwararu tafiyar da aikin gina sabon ofishin hukumar aikin kula tafiyar da gina akan kudi naira miliyan 45 wanda yanzu aikin ya kai kashi 96 cikin dari wato dai ana gaba da kammala shi. Kuma ya ce sun ba ma’aikatan hukumar horo a lokuta daban daban wanda ya ci kudi har naira miliyan 16
Ta bangaran tattara haraji kuma ya ce sun yi kokari so sai, inda ya ce a shekarar 2020 sun tara fiye da biliyan 9 sai kuma a shekarar 2019 sun tara fiye da biliyan 8 sai kuma shekarar 2018 sun tara biliyan 6 sannan suka tara biliyan 5 a shekarar 2017.
“Yanzu haka wannan hukuma ta mu tana da ma’aikata akalla 205 sannan mun dauki ma’aikatan wucin gadi guda 110 kuma mun samu nasarar sayan motoci har guda 14 tare da mashina 35 domin samun damar tafiyar da aikin wannan hukuma cikin nasara ba tare da wani tarnaki ba” in ji shi.