Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi,
Gwamnatin jihar Kebbi a jiya ta baiwa al’ummar Fulani 2,778 tallafin Dabbobin da kuma abinci domin inganta rayuwar su a duk fadin jihar ta Kebbi.
An kaddamar da bikin bada tallafin ne a rugar Hulkui da ke a cikin karamar hukumar Mulki ta Maiyama a jihar ta Kebbi a jiya, inda Fulanin yankin na karamar hukumar mulki ta Maiyama sun samu tallafin Tumaki da raguna da kuma abincinsu, haka kuma wasu sun samu shanun yin madara da abin da kuma kudi Naira dubu arba’in da kuma wayar hannu domin a rika sanin yanayin da dabbobin da aka basu suke ciki.
Dabbobin da aka bayar a wurin taron bikin sun hada da Tumaki, Awaki, Kaji da kuma Shanu, Sai abincin dabbobi da kuma kaddamar da tsarin yin madara ga Matan Fulani makiyaya wato (Yoghurt) har da kuma tsarin karbar madarar da za su samar ga hannun matan na Fulani makiyaya .
Tallafin dai wata hanya ce da gwamnatin jihar Kebbi ta fito da ita a matsayin wani shiri na bada tallafin na bashi ga al’ummar Fulani makiyaya domin karfafawa da kuma inganta rayuwar Fulani makiyaya na jihar a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu tare hadin gwiwar ma’aikatar kula da dabbobi da kuma kiwon kifi ta jihar ta taimakon kungiyar Fulani wato Miyelti-Allah reshen jihar ta Kebbi domin tabbatar da cewa Fulani makiyaya a jihar sun kara samun sana’o’in da za su dogaro da kansu, wanda hakan wata dama ce ta a de na yi wa al’ummar Fulani kallon ‘yan ta’adda ko masu hannu daga cikin aikata miyagun laifufuka a jihohin kasar nan.
Da yake jawabi a wurin taron bikin kaddamar da bada tallafin dabbobi ga Fulani makiyaya na karamar hukumar Mulki ta Maiyama, Kwamishinan ma’aikatar Kula da dabbobi da kiwon kifi, Aminu Garba Dandiga ya bayyana cewa” gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, a matsayina na Kwamishinan ma’aikatar Dabbobi akwai tsari guda bakwai da aka fito dashi wanda na bada tallafi ga Fulani makiyaya na duk fadin jihar, bisa ga hakan ne zamu kaddamar da tsarin
guda daya a wannan karamar hukumar ta Maiyama wanda rugar Hulkui ne za a kaddamar da tsarin kuma su ne zasu ci gajiyar tsarin da gwamnatin jihar Kebbi ta fito dashi, inji Kwamishinan ma’aikatar Dabbobi da kiwon kifi Alhaji Aminu Garba Dandiga yayin gabatar da jawabinsa”.
Haka kuma ya ci gaba da cewa” duk mutunen da ke cikin tsarin kiwon Tumaki, kowane mutun guda za a bashi Tunkiya biyu da rago da kuma abincinsu domin yayi kiyo ido suka haihu za a karba a ba na kusa gare shi domin shi ma ya ci gajiyar. Sai kuma mutanen da ke cikin tsarin kiwon Awaki da Kaji suma tsarin su daya ne. Amma masu samar da madarar Yoghurt za su raba riba ne gida biyu sai su bada kashi daya su kuma su amfana da kashi daya, inji shi”.
Haka kuma wakilinmu ya samu jin ta bakin daya daga cikin matan fulani makiyaya da ta samu nasarar ci gajiyar tsarin maisuna Aisha Muhammad ta ce” muna godiya ga gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da kuma Kwamishinan ma’aikatar Dabbobin Alhaji Aminu Garba Dandiga kan irin wannan tallafi da aka basu. Ta kuma bada tabbacin cewa zasu yi amfani da wannan tallafi da aka basu domin kara inganta rayuwar su ta hanyar yin sana’ar kiwon Tumaki da kuma kaji, inji Aisha Muhammad da ke a rugar Hulkui ta garin Maiyama”.