Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi za ta raba injinan sussuka gero da masara da dawa ga ƙungiyoyin mata da kuma mata masu aikin Sussukar gero, masara da ka dawa musamman a yankunan karkara.
Bayani na kumshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labarai na Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Mu’azu Dakingari da ya sanya wa hannu, ya ce, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya sanar da hakan ne yayin da yake tattauna wa da matan da ke sussuka a karkara ta hanyar sa ta zuwa garin Dolekaina da Tungar Sule da Fingilla da Kyangakwai, dukkansu a cikin karamar hukumar mulki ta Dandi da ke jihar.
Bayan tattaunawar Gwamnan ya shawarce su da su kafa ƙungiyoyi mata na manoma don samun damar taimakon kudi domin inganta tattalin arzikinsu.
Daga nan Sanata Bagudu ya ziyarci garin Fingilla da Dandi, inda ya bukaci Fulani da makiyaya su inganta zaman lafiya tsakaninsu, “fahimta da ƙauna ga juna tare da manoma a jihar don kauce wa rikici” in ji shi.
Daga bisani ya fada musu cewa, su rubuto dukkan bukatunsu ta hanyar shugabannin su na gari wanda za su mika wa gwamnati domin daukan mataki.