Abubakar Abba">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Gwamnatin Kwara Ta Gano Gibin Da Ake Da Shi A Bangaren Noman Waken Soya

by Abubakar Abba
January 4, 2021
in NOMA
3 min read
Noman Waken Soya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Duk da yawan noman waken soya da ake yi a jihar Kwara, Gwamnatin jihar ta bayyana cewa, ta gano gibin da take da shi a bangaren noman waken soya.

Kwaminshinan ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta jihar Alhaji Muritala Olarewaju ne ya bayyana hakan a lokacin kadammar da shirin habaka aikin nomad a rage yin dogaro kan mai na (OSOP) da aka gudanar a garin Ilorin.

samndaads

Alhaji Muritala Olarewaju ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar ta kan yin kokari wajen bunkasa noman waken soya a jihar, musamman domin cimma bukatar wadatar da jihar da waken soya da kuma kai shi kasuwanni.

Kwaminshinan ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta jihar Alhaji Muritala Olarewaju ya kuma jaddada aniyar gwamnatin gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazak wajen ci gaba da tallafa wa manoman a jihar ta hanyar samar masu da igantaccen takin zamani da sauran kayan aikin noma.

Kwaminshinan ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta jihar Alhaji Muritala Olarewaju ya kuma yaba wa hukumar da luar da fitar da amfanin gona zuwa kasar waje (NEPC) kan rawar da ta ke taka wa wajen ganin an fitar da ingantaccen amfanin gona daga kasar nan zuwa kasashen waje.

Shi ma a sakonsa na Fatah alheri a taron, Darkta kuma babban jami’I a hukukar ta (NEPC), Mista Olusegun Awolowo, ya tunasar da mahalarta taron cewa, tun kafin a gano mai a shekarar 1957, fannin aikin noma shi ne ginshikin habaka tattalin arzikin kasar nan, inda ya yi nuni da cewa, fannin ya na samar da kashi 65 a cikin dari na tattalin arziki tare da kuma samar da ayyukan yi sama da kashi 85 a cikin dari na yawan alummar da ke kasar nan.

Awolowo, wanda ya sanar da hakan ta hanyar Mista Olu Ikulajolu ya yi nuni da cewa, bangaren noma na kasar ya fara rawa ne tun a shekarar that the 1970 bayan da aka gano mai, inda hakan ya sanya gwamnatocin das u ka gabata, su ka mayar da hankulansu kan man domin samun kudaden shiga masu ya wa.

Darkta kuma babban jami’I a hukukar ta (NEPC), Mista Olusegun Awolowo ya ci gaba da cewa, saboda raguwar da aka samu kan gudunmawar da fannin aikin noman kasar ke samar wa tattalin arzikin kasar, hakan ya sa hukumar ta (NEPC) ta samar da wani kundi a shekarar 2015 domin a rage dogaro kan mai.

Mista Olusegun Awolowo ya sanar da cewa, shirin ya taimaka waje samar da dabaru kan yadda za a kara samar da kudaden musaya na kasar waje ta hanyar rashin dogaro da fannin samar da mai.

A cewar Mista Olusegun Awolowo, kafin samar da kundin hukumar ta NEPC ta yi hadaka da kan shirin na Product (OSOP), inda ya yi nuni da cewa, manufar ita ce, domin sauran jihohin a kasar nan su ma su shiga a dama da su wajen bunkasa fitar da amfanin gona zuwa kasar waje.

Awolowo ya kara da cewa jihar Kwara tuni ta nuna sha’awarta na habaka noman waken soya kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin, suna bayar da gagarumar gudunmawa.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Masu Sarrafa Rogo Sun Bukaci A Bunkasa Shirin BCDP

Next Post

Dalilin Dan Majalisa Na Tallafa Wa Wasu Matasa A Mazabarsa Da Jarin Kiwon Zomo

RelatedPosts

Shanu

Manyan Motoci 60 Ke Zuwa Kasuwar Sayar Da Shanu Ta Wudil A Duk Sati

by Abubakar Abba
20 hours ago
0

Akwai ksauwannin sayar da Shanu da dama a Nijeriya, amma...

Rogo

Muna Bukatar Takin Zamani –Manoman Rogo A Kwara

by Abubakar Abba
5 days ago
0

Manoman Rogo a jihar Kwara sun yi kira ga gwamnatin...

Kananan Manoma

Kananan Manoma Sun Bukaci Bashi Daga CBN

by Abubakar Abba
5 days ago
0

Wasu daga cikin kananan manoman a kasar nan, sun bukaci...

Next Post
Kiwon Zomo

Dalilin Dan Majalisa Na Tallafa Wa Wasu Matasa A Mazabarsa Da Jarin Kiwon Zomo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version