Daga Sulaiman Ibrahim,
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ‘yan mata musulmi da ke son shiga makarantun gwamnati a kowane fanni na makarantun gwamnati suna da ‘yancin sanya hijabi zuwa makaranta.
Kwamishiniyar ilimi da ci gaban bil Adama ta jihar Hajia Sa’adatu Modibbo Kawu ce ta bayyana hakan a lokacin wani taron zaman lafiya da masu ruwa da tsaki na musulmi da kirista a garin Ijagbo dake karamar hukumar Oyun ta jihar.
Don haka ta yi kira ga shugabannin Musulmi da Kirista da su hada kai don habbaka zaman lafiya a jihar.
Ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana kokarin kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar zai fuskanci fushin doka.
Taron ya samu halartar sakatariyar dindindin, Misis Mary Adeosun; shugaban hukumar hidimar koyarwa, Alhaji Taoheed Bello; shugabannin hukumar kula da ayyukan koyarwa; shugaban kungiyar shugabannin makarantun sakandire ta Nijeriya (ANCOPSS), Alhaji Toyin Abdullahi; da shugaban kungiyar malamai ta Nijeriya (NUT), Alh Umar Abdullahi.