Bala Kukuru" />

Gwamnatin Na Shirye-Shiryen Farfado Da Noma A Katsina

Shugaban kungiyar manoman jihar Katsina Alhaji Tukur na  Dantsoho Kankara , ya nuna yabawarsa game da shirye-shiryen gwamnatin taraya da gwamnatocin jihohin kasar nan wajen farfado da harkokin noma a kowace jiha.

Shugaban ya ci gaba da cewa “manoman kasar nan suna da kyakyawar rawar da ya kamata su taka na kara bunkasa kasar nan da abinci idan har gwamnatoci suka ci gaba da tallafawa harkar noma. babu shakka za ta kara samun farfadowar tatalin arziki  da kuma kara samun yalwatar abinci da sauran abubuwan jin dadin rayuwa.

Tukur ya kara da cewa a kan haka ne yake kiran ga manoman jihar Katsina da sauran manyan jihohin kasar nan da su tashi tsaye wajen gudanar da harkokin noma domin kara bunkasa kasar nan da abinci.

A cewarsa tun da gwamnatocin kasar nan sun tsaya tsayin daka wajen tallafa wa manoman rani da damuna sannan ya kara da cewa ya kamata su ma manya manoman kasar nan su rinka samun irin wannan tallafi na takin zamani da irin shuka mai kyau da maganin feshin ciyawa da na kwari da motocin noma da sauran makamantansu. A cewarsa yana ba gwamnati shawara a kan wannan al’amari  zai sa gwamnatin ta cim ma burinta na habaka kasar nan da abinci.

Sannan ya kara da cewa, ya ba kungiyoyin manoma shawara da sauran al’umma musamman masu karbar bashi ko tallafin da gwamnatoci ke bada wa ga manoma  da zummar idan locakin da aka diba za a biya to don Allah mutane a yi kokari a biya. Hakan shi zai ba gwamnati kwarin gwiwar sake bullo da wasu shirye-shiryen tallafa wa harkar noma.

Sannan ya kara da cewar suna ci gaba da yi wa wannan gwamnatin addu’o’in alheri domin samun nasarar gudanar da ayyukan ciyar da kasar nana gaba.

Daga nan sai ya bayar da shawa ga ‘yan Nijeriya da su kara ba shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya saboda ya sake dawo wa domin ya karasa ayyukan da yake yi wa kasar nan .

Haka kuma ya ce, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi wa wannan gwamnati uzuri,  idan aka duba yadda gwamnatin ta kawo zaman lafiya a kasar nan. Domin zaman lafiya shi ne kan gaba da komai.

Exit mobile version