Gwamnatin Nasarawa Na Shirin Daukar Mataki Kan Masu Bahaya A Fili

Fili

Daga Ahmed Muhammed Danasabe, 

Kwamishinan tsaftar muhalli na Jihar Nasarawa, Alhaji Musa Abubakar, ya fadi hakan, a sa’ilin da  yake zantawa da manema labarai bayan kammala dokar shara ta karshen watan yuni.
Yace, gwamnatin Jihar Nasarawa za ta bi kudurin shugaban kasa  Muhammadu Buhari da ya ayyana nan da shekarar 2025 ya kasance babu gudanar da bahaya a fili.
Ya ce, burin gwamnati, shi ne  kowane gida su mallaki matsuguni saboda bahaya.
A cewarsa, yanzu ana samun saukin tsaftar muhalli saboda al’ummar Jihar Nasarawa sun fahinci wannan tsarin sun gudanar da tsaftar muhalli da dakatar da zirga-zirga a wannan rana.
Kwamishinan ya kuma ce mutum goma sha daya ne aka kama, kuma ‘yan acaba ne, wadanda za a gabatar dasu gaban kotun tafi da gidanka, a yi musu hukunci na tara ko gidan yari.
Ya kara da cewa duk da yajin aiki da wasu ma’aikatan ke yi, shi a ma’aiktansa, ma’aikatan sun fito aiki kamar yadda aka saba.
Alhaji Musa Abubakar ya kuma godema al’ummar Jihar Nasarawa da suke baiwa gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule goyon baya wajen gudanar da tsaftar muhalli a cikin Jihar .
Motocin tsaftar muhalli sun bazama wajen kwashe shara a duk guraren da ake zuba shara babu wani matsala ko alama daya nuna ana yajin aiki a Jihar ta Nasarawa.

Exit mobile version