Daga Zubairu T.M. Lawal, Lafia
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta nuna takaicinta ta yadda wasu masu horar da ‘yan wasan kwallon kafa da sauransu na jihar ke yin handama da baba-kere a albashin ‘yan wasa.
Da yake zantawa da manema Labarai, Kwamishinan wasanni na jihar, Hon. Bamaiyi Anangba ya ce; abin takaici ne yadda kodayaushe ‘yan wasan jihar ke kukawa cewa Gwamnati ba ta biyansu albashi na tsawon watannin kaza ko kaza ba.
Ya ce akwai mutanen da mukaminsu ya wuce su zauna a wannan kurbin, amma sun ki zuwa saboda yadda ake facaka da dukiyar Gwamnati. Ya ce; duk da kudin da Gwamna Umar Tanko Al-makura yake kashewa na ganin ci gaban wasanni a wannan Jihar, amma an samu marasa kishi suke handamewa.
Kwamishinan ya ce; “yadda muka gano wannan matsalar, shi ne ana biyan albashi a tebur ne, hannu da hannu, sai mai horar da ‘yan wasan mutum daya ya karbi na yara hudu , wannan ya karbi na yara biyu da nufin cewa zai kai masu.”
Ya ce; “dalilin haka ne suka dauki matakin magance wannan matsalar ta hanyar biyan kowa albashinsa ta banki, kama daga ‘yan wasa har masu horar da su, kowa ya je ya bude asusun ajiya a banki ya zo da takardunsa da numbobin ajiyarsa da zarar wata ya yi za a rika sanya masa kudinsa ta nan. Kuma wannan matsalar tana cikin dukkan kungiyoyin wasanninmu na jihar.”
Ya ci gaba da cewa; “wannan matsalar ta sanya ‘yan wasan Nasarawa United da farko sun ki sake jiki su buga kwallo, amma da muka daura damarar yaki da wannan al’mundahanar, sai ga shi sun kasance masu samun nasara a wasanni. Tun da aka fara buga wasan Firimiya na Kasa .yan wasanmu ba su yi rashin nasara a gida ba, sau daya suka yi kunni doki da kungiyar ‘yan wasan Gombe United. Sannan sun je sun rike wasu kungiyoyi na waje kunnin doki ko nasara.”
Ya ce kalubalen da kungiyar wasan ta Nasarawa United ta samu shi ne bai wuce matsayin da ta kai ba duk da cewa ana ganin ta yi kokari, amma kalubalen da ke gabanta, shi ne ta dubi ‘yan wasan Plateu United, wanda a baya ko labarinsu ba a ji saboda rashin tabuka komai tsawon shekaru hudu, amma yau su ne suka zama zakarun wasanni na Kasa.