A ranar Alhamis din da tagabata ne Gwamnanan Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura tare da tawagarsa suka isa sansanin ’yan gudun hijira da ke garin Kadarko da ke yankin raya kasa na Giza cikin Karamar hukumar Keana. Gwamnan ya isa garin Kadarko tare da kayayakin masarufi, haka zalika daga kadarko ya kara zuwa garin Agyaragu inda nan ma sansanin ’yan gudun hijira ne da suka tare a makarantun Firamare. Wadanan ’yan gudun hijira sun kasance a makarantun Firamare ne tun lokacin rikicin da ya barke da manoma, Ya barke bayan ayyana dokar kiwo a killace wanda Gwamnatin Benuwe ta ayyana.
Da yake bayani ga ’yan gudun hijirar, Gwamna Umar Tanko Al-makura, ya yi kira gare su da su kasance masu hakuri da juna. Tun bayan wannan rikicin da ya faru a Benuwe wasu suka yi kokarin shigo da rikicin cikin Jihar Nasarawa amma Gwamnatin jihar Nasarawa ta tsaya a tsaye ba ta bari wannan rikicin ya yi tasiri a jihar ba. “Mun yi amfani da Jami’an tsaro a kan lokaci, saboda kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Kuma muka kawo wa ’yan gudun hijira dauki na gagawa irin kayayakin da zai kare lafiyansu da abinci da magunguna da sauransu, muka tsugunar da su a guraren da ya dace”.
Gwamnan ya ce, “wannan kayayakin da muka sake kawo maku wanda ya ha]a da katifa Zannuwa, Yaduka da Madara. Bargo, Suga, Magi, Audugar Mata, Masara, Wake, Taliya, Indomi da sauransu, za su tare mako wasu ’yan matsaloli. Sannan za mu bukaci tunda yanzu an kara yawan jami’an tsaro kuma komai ya lafa Jami’an tsaro za su kasance tare da ku a garuruwanku. Idan kun koma muna bukatar ku baiwa Jami’an tsaro hadin kai ku yi aiki tare”.
Da yake zantawa da manema Labarai, Gwamna Umar Tanko Al-makura ya ce, “tunda yanzu mun ga yanayin an samu zaman lafiya a guraren da ’yan gudun hijirar suka gudo kuma mun sanya jami’an tsaro kota ina, kauyuka da ko’ina muna da tabbacin zaman lafiya ya samu. Saboda haka muke ganin wannan gurin da ’yan gudun hijirar suke zaune ba wuri ne da ya dace da sansanin ’yan gudun hijira ba. Tunda makaranta ce kuma yanzu zafi ya yi yawa yadda suke kunshe a guri daya sai ka ga wasu cutuka sun bullo sun kawo wata illa. Saboda haka muke ganin tunda an samu zaman lafiya babu abin da ya fi kamar su koma gurarensu, tunda yanzu mun zuba jami’an tsaro ko ta ina. Yanzu nan da kwanaki kadan za a fara ruwan sama kuma mutanen nan manoma ne, idan suna zaune nan ba za su ji dadi ba, hankalinsu zai koma gida kuma komai dadin da kake ji a wani gida zaman gidanka na kanka ya fi shi. Saboda haka muka kawo wanan kayan na tallafi muka taimaka masu wadanda suke zaune a Kadarko da na nan Agyaragu. Kuma Gwamnati za ta taimaka masu su gyara muhallinsu saboda su koma su zauna su yi noma”.
A dai garin Kadarko bayan kayayakin Masarufi cikin manyan motoci guda biyu, an taimaka masu da kudi Naira miliyon biyar. Suma masu gudun hijira a Agyaragu bayan kayayakin masarufin an ba su Naira miliyon biyu.