Daga Bello Hamza,
Gwamnatin jihar Nasarawa ta gargadi masu sare itatuwa da kuma makiyaya da cewa kada su mamaye gandun dajin jihar da kuma wuraren bude ido na Farin Ruwa da ke jihar.
Kwamishinan al’adu da yawon bude ido, Mr Dogo Shammah, ya yi wannan gargadin a ranar juma’a a yayin da ya ziyarci wurin yawon bude na Farin Ruwa da ke karamar hukumar Wamba.
Kwamishina Shammah ya kai ziyarar ne tare da Mr Musa Abubakar, kwamishinan muhalli da albarkatun kasa.
Ya kuma bayyana cewa, kare gandun dajin na daga cikin manufofin gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule na samar wa jihar wasu hanyoyin samar da kudin shiga don yi wa al’umma aiki.